Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da gaskiya, kuma ya bada labarin cewa lazimtarta yana kaiwa zuwa aiki na gari madawwami, mai lazimtar aikin alheri yana kai mai shi zuwa ga aljanna, ba zai gushe ba gaskiya tana mai maituwa ga reshi a boye da fili, kuma yana cancantar sunan mai yawan gaskiya; shi ne kai matuƙa a gaskiya, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tsawatar daga ƙarya da faɗar ƙarya; domin cewa ita tana kaiwa zuwa karkacewa daga daidai da kuma aikin sharri da ɓarna da saɓo, sannan ta kaishi zuwa wuta, ba zai gusheba yana yawaita ƙarya har sai an rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah.
- Gaskiya ɗabi'a ce mai girma tana samuwa ne ta hanyar aiki da ƙoƙari, domin cewa mutum ba zai gusheba yana gaskiya kuma yana kardadon gaskiya, har sai gaskiya ta zama ɗabi'a gare shi, sai a rubuta shi a wurin Allah cikin masu yawan gaskiya kuma mutanen kirki.
- Ƙarya ɗabi'a ce abar zargi mai ita yana samuntane saboda tsawon gogayyarsa, da kardadonsa a faɗa da aikatawa, har sai ta wayi gari ɗabi'a, sannan a rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Gaskiya ana fadinta ne akan gaskiyar harshe, ita ce kishiyar ƙarya, da gaskiya a niyya ita ce ikhlasi, da gaskiya a ƙudirin niyya akan alheri da ya yi niyyarsa, da gaskiya a cikin ayyuka, mafi ƙarancinta daidaituwar zahirinsa da badininsa. Da gaskiya a matakai, kamar gaskiya a tsoro da ƙauna da wasunsu, wanda ya siffantu da hakan to ya zama mai yawan gaskiya, ko (ya siffantu) da wasu daga cikinsu to ya zama mai gaskiya.
صحيح البخاري (8/ 25) (6094). صحيح مسلم (4/ 2013) (2607). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 479). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 313). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 417). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، لمحمد الصنعاني (2/ 686).