Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda aka haramtawa sauƙi to ba'a datar da shi ba a cikin al'amuran addini dana duniya haka da cikin abinda yake tasarrufi a cikinsa ga kansa, da kuma abinda yake tasarrufi a cikinsa tare da waninsa, to haƙiƙa an hana masa alheri gabaɗayansa.
- Falalar sauƙi da kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da shi, da zargin tsanani.
- Sauƙi da shi ne aka samu tsarin alkairan duniya da lahira da yalwatuwar al'amuransu, a kwai kishiyar hakan a cikin tsanani.
- Sauƙi mai fitowane daga kyawawan ɗabi'u da zaman lafiya, shi kuma tsanani mai fitowane daga fushi da zafin zuciya, saboda hakane tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi yabo ga sauƙi kuma ya zurfafa a cikinsa.
- Sufyanus Sauri - Allah Ya yi masa rahama - ya cea almajiransa: Shin kun san menene sauƙi? shi ne ka sanya al'amura a bigiransu, tsanani a bigiransa, laushi a bigiransa, takobi a bigiranta, bulala a bigiranta.
صحيح مسلم (4/ 2003) (2592). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 532). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص416). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 592). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (9/ 152). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 687). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (6/ 241).