Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ka yi fushi

عن أبي هريرة رضي الله عنه: أَنَّ رَجُلًا قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَوْصِنِي، قَالَ: «لَا تَغْضَبْ» فَرَدَّدَ مِرَارًا قَالَ: «لَا تَغْضَبْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ɗaya daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - ya nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da shi a kan wani abin da zai amfaneshi, sai ya umarceshi da kada ya yi fushi, ma'anar hakan cewa shi ne ya nisanci sabubban da za su sa shi fushi, kuma ya tsare kansa idan fushi ya faru gareshi, kada ya zarce tare da fushinsa da kisa ko duka ko zagi da makamancin hakan. Mutumin ya maimaita neman wasiyya da yawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai ƙara komai a wasiyyarsa ba a kan "Kada ka yi fushi".

Fa’idoji
  1. Gargaɗi akan fushi da sabubbansa, domin cewa shine matattarar sharri, kiyayarsa shi ne matattarar alheri.
  2. Yin fushi saboda Allah; kamar fushi a lokacin keta alfarmomin Allah ya na daga fushi abin yabo.
  3. Maimaita zance a lokacin buƙata har mai ji ya kiyayeshi ya riski muhimmancinsa.
  4. Falalar neman wasiyya daga malami.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 28) (6116). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص36). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص181). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص64). المعجم الوسيط، (2/ 1038). تاج العروس من جواهر القاموس، للزبيدي (3/ 485).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com