Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u

‌عَنْ ‌أَبِي ‌ذَرٍّ، ‌جُنْدُبِ ‌بْنِ ‌جُنَادَةَ، ‌وَأَبِي ‌عَبْدِ ‌الرَّحْمَنِ، ‌مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «اتَّقِ اللَّهَ حَيْثُمَا كُنْت، وَأَتْبِعْ السَّيِّئَةَ الْحَسَنَةَ تَمْحُهَا، وَخَالِقْ النَّاسَ بِخُلُقٍ حَسَنٍ».
Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaTirmizi ya ce Hadisi ne Hasan
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.

Fa’idoji
  1. Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga bayi a kan rahamarSa da gafararSa da kuma rangwaminSa.
  2. Hadisin ya ƙunshi haƙƙoƙi uku: Haƙƙin Allah da taƙawa, da haƙƙin rai ta hanyar aikata kyawawan halaye bayan munanan (halaye), da kuma haƙƙin mu'amala ta hanyar aikata kyawawan ɗabi'u.
  3. Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan (halaye) bayan munanan (halaye), da kyawawan ɗabi'u, na ɗabi'un tsoron Allah, kawai an ambace su da ambato ne dan buƙatuwa zuwa ga bayaninsu.
Madogara

الأربعون النووية (ص100) (ح18). سنن الترمذي (3/ 526) (1987). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص40). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص195). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، لعبد المحسن البدر (ص67).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HALAYE NAGARI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com