Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike

عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَوْ أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَوَكَّلُونَ عَلَى اللهِ حَقَّ تَوَكُّلِهِ لَرَزَقَكُمْ كَمَا يَرْزَقُ الطَّيْرَ تَغْدُو خِمَاصًا وَتَرُوحُ بِطَانًا».
Daga Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike».
Imam Ahmad da Tirmithi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa da kuma Hakim ne Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwaɗaitar da mu da cewa mu dogara ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - wajen jawo amfani da tunkuɗe cuta a al'amuran duniya da Addini, domin cewa ba mai bayarwa, ba mai hanawa, ba mai cutarwa, ba mai amfanarwa sai shi - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka-, kuma mu aikata sabubban da za su jawo mana amfani su tunkuɗe mana cuta tare da gaskiyar dogaro ga Allah, a duk lokacin da muka aikata haka Allah Zai azurtamu kamar yadda Yake azurta tsuntsun da yake fita da safe alhali yana a yunwace, sannan ya dawo da yamma alhali cikinsa a cike, wannan aikin daga tsuntsu wani nau'i ne daga sabubba a tafiya don neman arziki, ba tare da ƙaryar dogaro ba da kuma kasala.

Fa’idoji
  1. Falalar dogaro ga Allah, kuma yana daga mafi girman sabubban da ake jawo arziki da su.
  2. Tawakkali ba ya kore sabubba, domin ya ba da labarin cewa tawakkali na haƙiƙa jijjifi da yammaci a neman arziki ba ya kishiyantarsa.
  3. Himmatuwar shari'a da ayyukan zuciya; domin dogaro aiki ne na zuciya.
  4. Rataya da sabubba kawai tawaya ne a addini, barin sabubba kuma tawaya ne a hankali.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 151) (2344). سنن ابن ماجه (5/ 266) (4164). مسند أحمد (1/ 332) (205). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص103). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص152). الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله المحسن (ص91).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN AYYUKAN ZUCIYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com