Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ وَعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «مَا يُصِيبُ الْمُسْلِمَ مِنْ نَصَبٍ وَلَا وَصَبٍ وَلَا هَمٍّ وَلَا حُزْنٍ وَلَا أَذًى وَلَا غَمٍّ حَتَّى الشَّوْكَةِ يُشَاكُهَا إِلَّا كَفَّرَ اللهُ بِهَا مِنْ خَطَايَاهُ».
Daga Abu Sa'id Alkhudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa abinda musulmi yake samu na cutuka da bakin cki da takaici da masibu da tsanani da tsoro da yunwa - kai koda akwai kayar da za ta taba shi ta sashi radadi -, hakan zai zama kaffara ga zunubansa da kuma kankare kurakuransa.

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar Allah ga bayinSa muminai da kuma rahamarSa garesu ta hanyar gafarta zunubai da mafi karancin cutar da zata samesu.
  2. Ya kamata ga musulmi ya nemi ladan abinda ya sameshi a wurin Allah, ya kuma yi hakuri akan dukkanin karami da babba, dan ya zama yana samun daukakar darajoji da kuma kankarewa ga munanan laifuka.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 114) (5641). صحيح مسلم (4/ 1992) (2572). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 489). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 242). شرح النووي على مسلم (16/ 126). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص44). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 96). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (1/ 70).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN TAUHIDI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com