Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

MANUFOFIN SHARI'A

Hadisai 3

Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina?

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَرَأَيْتَ إِنْ جَاءَ رَجُلٌ يُرِيدُ أَخْذَ مَالِي؟ قَالَ: «فَلَا تُعْطِهِ مَالَكَ» قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَاتَلَنِي؟ قَالَ: «قَاتِلْهُ» قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَتَلَنِي؟ قَالَ: «فَأَنْتَ شَهِيدٌ»، قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَتَلْتُهُ؟ قَالَ: «هُوَ فِي النَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina? Ya ce: «‌Kada ka ba shi kuɗinka)) Ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙe ni? Ya ce: «‌Ka yaƙe shi» Ya ce: Shin kana ganin idan ya kashe ni? Ya ce: «‌Kai shahidi ne». Ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi ? Ya ce: «‌Shi yana cikin wuta»
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son ƙwatar dukiyata? Ya ce: Bai wajaba ka miƙa wuya ka ba shi dukiyarka ba, ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙeni? Ya ce: Yana halatta gareka ka yaƙe shi, ya ce: Shin kana ganin idan ya kasheni fa? Ya ce: To kai shahidi ne, ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi fa? Ya ce: Shi ya cancanci a yi masa uƙuba a cikin wuta a ranar alƙiyama.

Fa’idoji
  1. Nawawu ya ce: Kare Mutuncin matar mutum (daga faɗe) wajibi ne ba tare da wani saɓani ba, kuma a sha'anin kare kai da kisa to akwai saɓani a cikin mazahabarmu (Shafi’iyyah) da mazahabar wasunmu, kare dukiya ya halatta amma ba wajibi ba ne.
  2. Hadisin dalili ne akan cewa lallai ilmi (ya zama) kafin aiki, inda wannan sahabin ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga abinda yake wajaba a kansa kafin ya aikata shi .
  3. Yana kamata abi a hankali a kare kai daga ɗan ta’adda, farko ta hanyar wa'azi ko neman agaji kafin fara kashe shi, idan ya fara yakar shi to lallai ƙoƙarinsa ya zama kare kai ne ba wai kisan ba.
  4. Jinin musulmi da dukiyarsa da kuma mutuncinsa to haramun ne.
  5. Nawawi ya ce: Ka sani cewa shahidi ya kasu gida uku; Na farkonsu wanda aka kashe a yaƙar kafirai, saboda wani sababi daga cikin sabubban yaƙi, to wannan yana da hukuncin shahidai a ladan lahira da kuma hukunce-hukuncen duniya, shi ne cewa ba za’a yi masa wanka ba kuma ba za’a yi masa sallah ba. Na biyu Shahidi a lada amma banda hukunce-hukuncen duniya, shi ne wanda ya mutu da ciwon ciki, da wanda aka kashe, da wanda gini ya faɗa masa, da wanda aka kashe dan kare dukiyarsa, da wasunsu daga waɗanda hadisai ingantattu suka zo da ambatansa shahidi, to wannan za’a yi masa, wanka za’a yi masa sallah, kuma shi a lahira yana da ladan shihidai, kuma baya lazimta ya zama yana da kwatankwacin ladan na farko. Na uku wanda ya saci ganima da makamancinta wanda hadisai suka zo da kore ambatansa shahidi idan an kashe shi a yaƙin kafirai, to wannan yana cikin shahidai a duniya, ba za’a yi masa wanka ba, kuma ba za’a yi masa sallah ba, kuma ba shi da ladansu cikakke a lahira.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 124) (140). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 449). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 936). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 389).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu.

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «ما نهيتكم عنه فاجتنبوه، وما أمرتكم به فأْتُوا منه ما استطعتم، فإنما أَهلَكَ الذين من قبلكم كثرةُ مسائلهم واختلافهم على أنبيائهم».
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah -Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana nuna mana cewa shi idan ya hanamu wani abu ya wajaba akanmu mu nisance shi ba tare da wata togaciya ba, kuma idan ya Umarcemu da wani abu kan mu yi shi to muyi gwargwadon iko sannan ya tsawatar mana don kada mu zamanto irin wasu Al'ummai da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawansu kuma suka saba musu sai Allah yayi musu Ukuba da Nau'o'in Hallaka da rusawa to ya dace kada mu kasance irin su don kada mu hallaka kamar yada suka hallaka.

Madogara

-التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، مطبعة دار نشر الثقافة، الإسكندرية، الطبعة: الأولى، 1380 هـ. -شرح الأربعين النووية، للشيخ ابن عثيمين، دار الثريا للنشر. -فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، دار ابن القيم، الدمام المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1424هـ/2003م. -الفوائد المستنبطة من الأربعين النووية، للشيخ عبد الرحمن البراك، دار التوحيد للنشر، الرياض. -شرح الأربعين النووية، للشيخ صالح آل الشيخ، دار الحجاز، الطبعة: الثانية، 1433هـ. -الأربعون النووية وتتمتها رواية ودراية، للشيخ خالد الدبيخي، ط. مدار الوطن. -الجامع في شروح الأربعين النووية، للشيخ محمد يسري، ط. دار اليسر. -صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. -صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى رُخَصُهُ، كَمَا يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى عَزَائِمُهُ».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa".
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana son azo wa rangwaminSa wadanda ya shara'antasu, na sauki a cikin hukunce-hukunce da ibadu, da saukakawa a cikinsu ga wanda aka dorawa shari'a - kamar kasarun sallah da kuma hada su a halin tafiya -. Kamar yadda cewa Shi Yana son azo wa azimarSa, daga al'amura wajibai; domin umarnin Allah a rangwame da wajibai daya ne.

Fa’idoji
  1. Rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayainSa, kuma cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - yana son a aikata abinda Ya shara'anta shi na rangwame.
  2. Cikar wannan shari'ar, da kuma dauke kunci ga musulmi.
Madogara

صحيح ابن حبان (2/ 69) (354)، فيض القدير (2/292)، نيل الأوطار (3/244).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com