Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCIN SHARI'A

Hadisai 5

Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake

عن النُّعمان بن بَشير رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ -وَأَهْوَى النُّعْمَانُ بِإِصْبَعَيْهِ إِلَى أُذُنَيْهِ-: «إِنَّ الْحَلَالَ بَيِّنٌ وَإِنَّ الْحَرَامَ بَيِّنٌ، وَبَيْنَهُمَا مُشْتَبِهَاتٌ لَا يَعْلَمُهُنَّ كَثِيرٌ مِنَ النَّاسِ، فَمَنِ اتَّقَى الشُّبُهَاتِ اسْتَبْرَأَ لِدِينِهِ وَعِرْضِهِ، وَمَنْ وَقَعَ فِي الشُّبُهَاتِ وَقَعَ فِي الْحَرَامِ، كَالرَّاعِي يَرْعَى حَوْلَ الْحِمَى يُوشِكُ أَنْ يَرْتَعَ فِيهِ، أَلَا وَإِنَّ لِكُلِّ مَلِكٍ حِمًى، أَلَا وَإِنَّ حِمَى اللهِ مَحَارِمُهُ، أَلَا وَإِنَّ فِي الْجَسَدِ مُضْغَةً، إِذَا صَلَحَتْ صَلَحَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، وَإِذَا فَسَدَتْ فَسَدَ الْجَسَدُ كُلُّهُ، أَلَا وَهِيَ الْقَلْبُ».
Daga Nu'umanu dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : - sai Nu'uman ya sakko da 'yan yatsunsa zuwa kunnuwansa -: "Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana wata ƙa'ida mai gamewa game da abubuwa, cewa sun kasu a shari'a zuwa kashi uku: Bayyanannen halal, da bayyanannen haram, da al'amura masu rikitarwa waɗanda hukuncinsu ba a bayyane yake ba ta bangaren halacci da haramci, da yawa daga mutane basa sanin hukuncinsu. Wanda ya bar waɗannan abubuwan masu rikitarwa gareshi, to, addininsa ya kuɓuta ta hanyar nisanta daga fadawa a cikin haram, kuma mutuncinsa ya kuɓuta daga zancen mutane da abin da za su dinga aibatashi a kansa saboda aikata wannan abin rikitarwar. Wanda bai nisanci shubuhohi ba, to, haƙiƙa ya kai kansa ko dai ga faɗawa a cikin haram, ko aibatawar mutane ga mutuncinsa. Kuma Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don ya bayyana halin wanda yake aikata shubuhohi, kuma cewa shi kamar mai kiwo ne da yake kiwon dabbobinsa kusa da ƙasar da mai ita ya sa mata shinge, dabbobin mai kiwon sun kusa su yi kiwon a cikin wannan shingen don kusancinsu gareshi, to, haka nan wanda yake aikata a bin da a cikinsa akwai shubha, to, shi da wannan ɗin yana kusantowa ga haram, kuma yana kusa da ya afka cikinsa. Bayan wannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa a cikin jiki akwai wata tsoka (ita ce zuciya) jiki yana gyaruwa da gyaruwarta, kuma yana ɓaci da ɓacinta.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan barin abu mai rikitarwa wanda hukuncinsa bai bayyana ba.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 20) (52). صحيح مسلم (3/ 1219) (1599). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثا النووية (ص18). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص105). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص41). فتح الباري لابن حجر (4/ 291). شرح النووي على مسلم (11/ 28).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An halatta muku Matattu guda biyu da jini guda biyu, amma Matattun sune Kifi da Fara, kuma Jinin shi ne Zuciya da Hanta

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «أُحِلَّتْ لكم مَيْتَتَانِ وَدَمَانِ، فأما الميتتان: فَالْجَرَادُ والْحُوتُ، وأما الدَّمَانِ: فالكبد والطحال».
Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "An halatta muku Matattu guda biyu da jini guda biyu, amma Matattun sune Kifi da Fara, kuma Jinin shi ne Zuciya da Hanta"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

1. توضيح الأحكام للشيخ البسام، ط5، مكتبة الأسدي، مكة المكرمة، 1423ه. 2. سُبل السلام، للصنعاني، دار الحديث. 3. تسهيل الإلمام، للشيخ صالح الفوزان، بعناية: عبدالسلام السليمان، ط1، 1427ه. 4. شرح الشيخ ابن عثيمين للبلوغ، تحقيق صبحي رمضان وآخر، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427ه. 5. منحة العلَّام للشيخ عبد الله بن صالح الفوزان، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1427ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah SAW ya sanya kwana Uku da daraensu ga mafiyi, da kuma Kwana xaya da Darensa ga mazaunin gida

عن شريح بن هانئ، قال: أتيتُ عائشة أسألها عن المسح على الخُفَّين، فقالت: عَلَيْكَ بِابْنِ أبِي طالب، فَسَلْهُ فإِنَّه كان يُسَافِرُ مع رسول الله صلى الله عليه وسلم فسألناه فقال: «جَعَلَ رسول الله صلى الله عليه وسلم ثَلَاثَةَ أَيَّامٍ وَلَيَالِيَهُنَّ للمسافر، ويوما وليلة للمُقيم».
L: Na zo wurin A’isha don na tambaye ta game da silifa a kan silifa, sai ta ce: Lallai ku yi da Ibn Abi Dalib, don haka ya tambaye shi, saboda yana tafiya tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi aminci - don haka muka tambaye shi, sai ya ce: “Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi masa kwana uku. Ga mazaunin».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Shurayh bin Hani daya ne daga cikin sahabban Ali - Allah ya yarda da shi - kuma ya zo wajen Ali - Allah ya yarda da shi - yana tambaya game da lokacin shafa kan safa, kuma wannan binciken ya kasance ne bayan mahaifiyarmu A’isha, Allah ku yarda da ita, sai ku tura shi zuwa ga Ali. Saboda shi masani ne a sunnar shafa, sai ya ce: (Mun tambaye shi game da shafa) wannan shi ne: game da tsawon lokacinsa, kuma shafawa rauni ne na jika a hannu ga memba, kuma silifas din takalmin fata ne wanda yana rufe duga-dugai, kuma sock shine nadewar mutum na kowane abu wanda ya kasance gashi ko ulu, mai kauri ko na bakin ciki, zuwa sama. Ana ɗaukar diddige don sanyi, kuma hukuncin daidai yake da takalmin yayin shafa Ali bin Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - ya ba su amsa: (Kwana uku da dararensu ga matafiyi, da yini daya da dare ga mazaunin.) A ciki akwai hujja ga abin da mafi yawan malamai suka tafi a kansa lokacin binciken ta kwana uku ga matafiyi, da rana daya da dare ga mazaunin, amma tsawon lokacin ya karu ga matafiyin. Saboda ya fi cancanta da izini fiye da mazaunin don wahalar tafiya.

Madogara

صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423 هـ. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة، الطبعة: الخامِسَة 1423هـ، 2003م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى رُخَصُهُ، كَمَا يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى عَزَائِمُهُ».
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa".
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana son azo wa rangwaminSa wadanda ya shara'antasu, na sauki a cikin hukunce-hukunce da ibadu, da saukakawa a cikinsu ga wanda aka dorawa shari'a - kamar kasarun sallah da kuma hada su a halin tafiya -. Kamar yadda cewa Shi Yana son azo wa azimarSa, daga al'amura wajibai; domin umarnin Allah a rangwame da wajibai daya ne.

Fa’idoji
  1. Rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayainSa, kuma cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - yana son a aikata abinda Ya shara'anta shi na rangwame.
  2. Cikar wannan shari'ar, da kuma dauke kunci ga musulmi.
Madogara

صحيح ابن حبان (2/ 69) (354)، فيض القدير (2/292)، نيل الأوطار (3/244).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْها قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا أَمَرَهُمْ أَمَرَهُمْ مِنَ الأَعْمَالِ بِمَا يُطِيقُونَ، قَالُوا: إِنَّا لَسْنَا كَهَيْئَتِكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّ اللَّهَ قَدْ غَفَرَ لَكَ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ، فَيَغْضَبُ حَتَّى يُعْرَفَ الغَضَبُ فِي وَجْهِهِ، ثُمَّ يَقُولُ: «إِنَّ أَتْقَاكُمْ وَأَعْلَمَكُمْ بِاللَّهِ أَنَا».
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarce su da wasu ayyukan yana umartar su da abin da zasu iya, suka ce: Lallai mu bamu kasance kamar yanayinka ba ya Manzon Allah, lallai Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: «Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa».
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarci mutane da wani aiki cikin ayyuka sai ya umarce su da abin da zai yi musu sauƙi banda wanda zai wahalar da su, dan jin tsoron kada su gajiya daga dawwama a kansa, sai ya yi aikin da shine kishiyar abin da yake umartarsu da shi daga sauƙaƙawa, sai dai cewa su sun nemi taklifin abin da zai wahalar da su daga gare shi, dan sun ƙudirce buƙatuwarsu zuwa kai matuƙa a cikin aikin dan ɗaukaka darajoji koma bayansa. Sai su ce: Lallai halinmu ba kamar halinka ba ne ya Manzon Allah, domin Allah haƙiƙa Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa, dan haka ku aikata abin da nake umartarku da shi.

Fa’idoji
  1. Ibnu Hajar ya ce: Kaɗai ya umarce su da abin da zai yi musu sauƙi ne dan su dawwama a kansa kamar yadda ya faɗa a ɗaya hadisn: «Mafi soyuwar aiki a wurin Allah mafi dawwamarsa».
  2. Mutum na gari yana kamata kada ya bar ijtihadi a cikin aiki dan dogaro akan shi mutumin kwarai ne.
  3. Halaccin mutum ya bada labarin halin da yake cikinsa na falala gwargwadan buƙatar hakan, in akwai aminci daga alfahari da kuma girmama kai.
  4. Abin da ya fi a cikin ibada shi ne tsakatsaki da kuma lazimta, ba wuce gona da iri ba wacce zata kai zuwa bari.
  5. Ibnu Hajar ya ce: Bawa idan ya kai ƙololuwa a cikin ibada da fa'idojinta hakan zai zama ya fi jansa zuwa lazimtarta, dan wanzar da ni'ima, da kuma neman ƙarinta ta hanyar godiya a kanta.
  6. Halaccin fushi yayin saɓawa al'amari na shari'a, da kuma yin inkari akan mai hazaƙa wanda ya dace ga fahimtar ma'ana idan ya taƙaita a cikin fahimtar, dan kwaɗaitarwa gareshi akan farkawa.
  7. Sauƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, kuma cewa Addini mai sauƙi ne, kuma cewa shari'a miƙaƙƙiya ce mai sauƙi.
  8. Tsananin kwaɗayin sahabbai a cikin ibada, da kuma yanda suke neman ƙarin alheri.
  9. Tsayuwa in da mai shara'antawa ya iyakance na Azima da kuma Rukhsa, da ƙudirce cewa riƙo da mafi sauƙi wanda ya dace da shari'a ya fi daga mafi tsanani wanda ya saɓawa shari'a.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 13) (20). شرح صحيح البخاري لابن بطال (73/1). عمدة القاري شرح صحيح البخاري (1/ 166).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com