عن أُمُّ سَلَمَة رضي الله عنها أن رسول الله صلى الله عليه وسلم سَمِعَ جَلَبَةَ خَصْمٍ بِبَابِ حُجْرَتِهِ، فَخَرَجَ إلَيْهِمْ، فقال: «ألا إنما أنا بشر، وإنما يأتيني الخصم، فلعل بعضكم أن يكون أبلغ من بعض؛ فَأَحْسِبُ أَنَّهُ صَادِقٌ؛ فَأَقْضِي لَهُ، فمن قضيت له بحق مسلم فإنما هي قطعة من نار، فَلْيَحْمِلْهَا أَوْ يَذَرْهَا».
Daga Ummusalama -Allah ya yarda da ita- cewa Manzon Allah tsira da aminci su tabbata agare shi ya ji hayaniyar husuma a kofar gidnsa sai ya fito wajen su, yace: "ku saurara lallai Ni mutum ne, tana yiwuwa masu husuma su zo min,kuma waninku ya fi wani iya magana, sai na yi tsammani shi ne mai gaskiya sai in bashi gaskiya to duk wanda na bashi gaskiya, alhali ba shi ne mai gaskiya ba, to ya sani yankin wuta ne, ko ya dauka ko ya bari,
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ji hayaniyar masu rigima,a kofar gidansa,sai ya fito don ya yi musu hukunci a tsakanin su sai yace: Lallai Ni mutum ne kamar ku, ban san gaibu ba, bana bada labarin boyayyayun al'amura, ban san waye mai gaskiya ko makaryaci a cikinku ba, masu rigima sukan zo dan na yi hikunci a tsakaninsu,kuma hukunci na yana kasancewa ne akan abin da na ji daga kowane bangare, da rantsuwoyinsu, kuma yana iya kasancewa wani yafi wani iya magana sai na zaci shi ne mai gaskiya sai na bashi gaskiya,tare da cewa abokin fadan shi ne mai gaskiya, ku sani ina hukunci da abubuwan da suke bayyane ne ba da wanda suke boye ba, ba zai halarta haram ba, don haka duk wanda na bawa gaskiya alhali ya san shi ne marar gaskiya, to yasan cewa wani yanki na wuta ne na yanko masa, in ya so sai ya dauka ko ya bari, sakamakon hakan na komawa akansa, Allah na jiran azzalumai a madakata
Madogara
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ.
تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ.
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ.
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَلَفَ عَلَى يَمِينٍ وَهُوَ فِيهَا فَاجِرٌ لِيَقْتَطِعَ بِهَا مَالَ امْرِئٍ مُسْلِمٍ، لَقِيَ اللَّهَ وَهُوَ عَلَيْهِ غَضْبَانُ». قَالَ: فَقَالَ الْأَشْعَثُ: فِيَّ وَاللَّهِ كَانَ ذَلِكَ؛ كَانَ بَيْنِي وَبَيْنَ رَجُلٍ مِنَ الْيَهُودِ أَرْضٌ، فَجَحَدَنِي، فَقَدَّمْتُهُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلَكَ بَيِّنَةٌ؟» قُلْتُ: لَا. قَالَ: فَقَالَ لِلْيَهُودِيِّ: «احْلِفْ». قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِذَنْ يَحْلِفَ وَيَذْهَبَ بِمَالِي. فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: {إِنَّ الَّذِينَ يَشْتَرُونَ بِعَهْدِ اللَّهِ وَأَيْمَانِهِمْ ثَمَنًا قَلِيلًا}. إِلَى آخِرِ الْآيَةِ.
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa".
ya ce: Sai Ash'As ya ce: Wallahi a kaina hakan ya kasance; ya kasance akwai wani fili tsakanina da wani mutum cikin Yahudawa, sai ya yi min musun filin, sai na kawo shi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce dani: "Shin kana da shaidu?" Na ce: A'a. Ya ce: Sai ya cewa Bayaahudan: "Ka rantse". Ya ce: Na ce: Ya manzon Allah, to sai ya rantse ya tafi da dukiyata. Sai Allah - Maɗaukin sarki - ya ce: {Lallai ne wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani farashi dan kadan}. har zuwa ƙarshen ayar,
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga yin rantsuwa tare da sanin mai rantsuwar cewa shi maƙaryaci ne a cikinta, dan ya ya karbi dukiyar waninsa; to zai gamu da Allah alhali Yana mai fushi da shi. Sai Ash'As ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa , Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi hakan lokacin da ya kasance akwai rigima ta mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum cikin Yahudawa, sai suka kai ƙara zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya cewa Ash'As: Wajibi ne ka zo da shaidun da suke tabbatar da abinda kake ƙararsa, idan ka kasa to baka da wani abu sai rantsuwar abokin rigimarka wanda ake ƙararsa, sai al-Ash'As ya ce: Ya manzon Allah, to bayahude zai rantse kuma ba ya taka tsantsan ya tafi da dukiya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da gasgata hakan a cikin Alƙur'ani a faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Lallai waɗanda suke musanya}.
Suke canja {da alƙawarin Allah}, da wasiyyarSa ga muminai da dawo da amana {da rantse-rantsensu} da rantsuwarsu da sunanSa suna maƙaryata {ɗan kudi kaɗan} na rabon duniya {To waɗannan basu da wani rabo a lahira} kuma basu da wani nasibi {Kuma Allah ba Zai yi musu magana ba}, da zancen da zai faranta musu rai ya amfanar da su ba, kai ya yi fushi da su, {Kuma ba Zai kallesu ba a ranar alƙiyama} kallo na rahama da kyautatawa, {Kuma ba Zai tsarkakesu ba} da yabo mai kyau ba, kuma ba Zai tsarkakesu da gafara daga zunubai da datti ba {Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a garesu} mai sa ciwo saboda abinda suka aikata.
Fa’idoji
- Hani daga halatta dukiyoyin mutane da ƙarya.
- Kaurara haƙƙoƙin musulmai a ƙanƙanin haƙƙi da mai yawansa.
- Shaidu suna kan mai kawo ƙara, rantsuwa kuma tana kan wanda aka kai ƙara idan ya musa.
- Tabbatar da haƙƙi da shaidu biyu, idan ba’a samu shaidu a wurin mai ƙara ba, to rantsuwa ta wajaba akan wanda aka kai ƙara.
- Haramta rantsuwa (mai dulmiyarwa) ita ce ta ƙarya wacce mai rantsuwa yake ƙwace haƙƙin waninsa da ita, kuma ita tana daga cikin manyan zunubai, wacce take bijirar da mai ita ga fushin Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma uƙubarSa.
- Shugaba ya yi wa abokanan rigima wa'azi, musamman ma a lokacin nufin yin rantsuwa.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 121) (2416).
صحيح مسلم (1/ 123) (138).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 136).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص687).
فتاوى اللجنة الدائمة - اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء (23/ 513).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه : أنه سمع رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: كانت امرأتان معهما ابناهما، جاء الذئب فذهب بابن إحداهما، فقالت لصاحبتها: إنما ذهب بابنك، وقالت الأخرى: إنما ذهب بابنك، فتحاكما إلى داود صلى الله عليه وسلم فقضى به للكبرى، فخرجتا على سليمان بن داود صلى الله عليه وسلم فأخبرتاه، فقال: ائتوني بالسكين أَشُقُّهُ بينهما، فقالت الصغرى: لا تفعل! رحمك الله، هو ابنها، فقضى به للصغرى.
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - cewa ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Mata biyu suna tare da 'ya'yansu maza, sai kerkeci ya zo ya tafi tare da dayan ɗayansu, sai ta ce wa kawarta: Ya tafi tare da ɗanka, ɗayan kuma ya ce: Ya je ga ɗanka, kuma sun yi ƙoƙari wurin Dauda - Allah ya yi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma ya zartar da shi ne ga babba, don haka suka fita zuwa wurin Suleiman bin Dawood - Allah ya kara masa yarda - suka gaya masa, sai ya ce: Kawo wukar a wurina ka raba su. Allah Ya yi muku rahama, shi danta ne, don haka ne ya hukunta shi ga karamar.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabinmu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba mu labarin labarin wasu mata biyu da suka fita tare da ‘ya’ya maza biyu, sai kerkeci ya cinye dan dayansu, dayan kuma ya kasance. Saboda babbansu na iya daina haihuwa, yayin da karamin yake karami kuma yana iya haihuwar wani a nan gaba, sai suka fita daga gare shi zuwa ga Sulaiman - amincin Allah ya tabbata a gare shi - dansa, sai ta ba shi labarin, don haka sai ya nemi wukar, ya ce: “Na yanke shi a tsakaninku. Dan na babba, tausayi da rahama sun ganeta saboda shine danta na gaskiya, don haka sai ta ce shi danta ne, ya Annabin Allah.
Madogara
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407هـ - 1987م.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، 1426هـ.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي.
صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ.
صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن ابنِ عباسٍ رضي الله عنهما أنَّ رسولَ اللهِ صلي الله عليه وسلم قال: «لَو يُعطَى النّاسُ بدَعواهُم لادَّعَى رِجالٌ أموالَ قَومٍ ودِماءَهُم، ولَكِنَّ البَيِّنَةَ على المُدَّعِى، واليَمينَ على مَن أنكَرَ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta".
Baihaki ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa da ace ana bawa mutane saboda kawai mujarradin da'awarsu ba tare da wasu dalilai ba ba kuma tare da wasu alamomi ba to da wasu mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanensu, sai dai gabatar da shaida da dalili ya wajaba akan mai da'awa da abinda yake nema, idan ba shi da shaidu to sai a gabatar da da'awar akan wanda aka kawo karar, idan ya yi inkarinta to ya wajaba ya yi rantsuwa sai ya kubuta.
Fa’idoji
- Ibnu Dakikil Id ya ce: Wanann Hadisin asali ne na hukunce-hukunce, kuma mafi girman makoma a lokacin jayayya da husuma.
- Shari'a ta zo dan kare dukiyoyin mutane da jinanensu daga wasa.
- Alkali ba ya hukunci da iliminsa kawai, yana komawa ne zuwa ga shaidu.
- Dukkan wanda ya yi wata da'awa wacce ta wofinta daga hujja to ita abar watsarwa ce, daidai ne ta kasance a cikin hakkoki ne da mu'amaloli ko a cikin mas'alolin imani da sani.
Madogara
السنن الكبرى للبيهقي تحقيق التركي (21/ 242 - 243) (21243).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص76).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص328).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، لعبد المحسن البدر (ص114).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن ابنِ عباسٍ رضي الله عنهما أنَّ رسولَ اللهِ صلي الله عليه وسلم قال: «لَو يُعطَى النّاسُ بدَعواهُم لادَّعَى رِجالٌ أموالَ قَومٍ ودِماءَهُم، لَكِنَّ البَيِّنَةَ على المُدَّعِى، واليَمينَ على مَن أنكَرَ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Da a ce ana bawa mutane abu saboda iƙirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta».
Baihaki da wasu suka ruwaito shi kamar haka, kuma sashensa yana cikin Bukhari da MuslimDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa da ace ana bawa mutane saboda kawai mujarradin da'awarsu ba tare da wasu dalilai ba ba kuma tare da wasu alamomi ba to da wasu mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanensu, sai dai gabatar da shaida da dalili ya wajaba akan mai da'awa da abinda yake nema, idan ba shi da shaidu to sai a gabatar da da'awar akan wanda aka kawo karar, idan ya yi inkarinta to ya wajaba ya yi rantsuwa sai ya kubuta.
Fa’idoji
- Ibnu Dakikil Id ya ce: Wanann Hadisin asali ne na hukunce-hukunce, kuma mafi girman makoma a lokacin jayayya da husuma.
- Shari'a ta zo dan kare dukiyoyin mutane da jinanensu daga wasa.
- Alkali ba ya hukunci da iliminsa kawai, yana komawa ne zuwa ga shaidu.
- Dukkan wanda ya yi wata da'awa wacce ta wofinta daga hujja to ita abar watsarwa ce, daidai ne ta kasance a cikin hakkoki ne da mu'amaloli ko a cikin mas'alolin imani da sani.
Madogara
السنن الكبرى للبيهقي تحقيق التركي (21/ 242 - 243) (21243).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص76).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص328).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، لعبد المحسن البدر (ص114).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com