Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashawa da mai ba da ita a hukunci

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: لَعَنَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الرَّاشِيَ وَالْمُرْتَشِيَ فِي الْحُكْمِ.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashawa da mai ba da ita a hukunci.
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mummnar addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a kan mai ba da rashawa da mai karɓarta. Daga hakan akwai abin da ake ba wa alƙalai don su yi zalunci a hukuncin da suke jiɓintarsa; don mai bayarwa ya kai ga manufarsa ba tare da wani haƙƙi ba.

Fa’idoji
  1. Ba da rashawa yana haramta, da karɓarta da yin hanya zuwa gareta, da taimako a kanta; don abin da ke cikinta na taimakekeniya a kan ƙarya (ɓarna).
  2. Rashawa tana daga manyan zunubai; domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓarta da mai ba da ita.
  3. Rashawa a shari'a (Alƙalanci) da hukunci ita ce mafi girman laifi, kuma mafi tsanani; don abin da ke cikinta na zalunci da hukunci ba tare da abin da Allah Ya saukar ba.
Madogara

سنن الترمذي (3/ 15) (1336). مسند أحمد (15/ 8) (9023). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، للبسام (7/ 188). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 172). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (9/ 450). سبل السلام شرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 577).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
LADUBBAN ALƘALI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com