Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تُقْطَعُ اليَدُ فِي رُبُعِ دِينَارٍ فَصَاعِدًا».
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ɓarawo ana yanke hannunsa saboda satar rubu'in dinari na zinare, da abinda ya ƙaru a kan hakan, kuma ya yi daidai da abinda ƙimarsa ta yi daidai da ƙimar 1.06 Gram na zinari.

Fa’idoji
  1. Sata tana daga cikin manyan zunubai.
  2. Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya iyakance uƙubar ɓarawo, ita ce yanke hannunsa; kamar yadda yake a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Barawo da ɓarauniya to ku yanke hannayensu} [al-Ma'ida: 38], kuma sunnah ta bayyana sharuɗɗan wannan yankewar.
  3. Abin nufi da hannu a cikin hadisin shi ne yanke tafi daga gaɓarsa tsakaninsa da tsakanin damtse.
  4. Daga hikima a cikin yanke hannun ɓarawo, (akwai) kiyaye dukiyoyin mutane, da tsawatar da waninsa (ɓarawon) cikin masu ta'addanci.
  5. Dinari awo ne na zinare, kuma ya yi daidai a yanzu da (4.25 KG) awon 24; to ɗaya bisa huɗu na dinari ya yi daidai da Gram da wani abu.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 160) (6789). صحيح مسلم (3/ 1312) (1684). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 125). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام، (ص665).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HADDIN SATA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com