Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCE-HUKUNCEN ABIN HAIHUWA

Hadisai 6

Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba]

عن ابن عمر رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنِ الْقَزَعِ.
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana aske wani sashi na kai da kuma barin wani sashin. Hanin gamamme ne ga Maza ƙanana da manya, amma ita mace ba ta da damar ta aske kanta.

Fa’idoji
  1. Kulawar Shari’ar Musulunci da yanayin [mutuntakar] mutum.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 163) (5921). صحيح مسلم (3/ 1675) (2120). نزهة المتقين (2/ 1126). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (19/ 380). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 381).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai ne mafi soyuwar sunayenku a wurin Allah (su ne) Abdullahi da Abdurrahman

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ أَحَبَّ أَسْمَائِكُمْ إِلَى اللهِ عَبْدُ اللهِ وَعَبْدُ الرَّحْمَنِ».
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai ne mafi soyuwar sunayenku a wurin Allah (su ne) Abdullahi da Abdurrahman".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar sunaye a wurin Allah su ne a ambaci namiji da: Abdullahi, ko: Abdurrahman.

Fa’idoji
  1. AlƘurɗubi ya ce: Za'a riskar da waɗannan sunayen a abinda ya kasance tamkarsu, kamar Abdurrahim da Abdulmalik da Abdussamad, kaɗai sun kasance mafi soyuwa zuwa ga Allah ne, domin cewa su sun ƙunshi abinda yake shi ne siffa ta wajibi ga Allah da abinda yake shi ne siffa ga mutum kuma wajibi gare shi, shi ne bauta, sannan aka raɓa bawa zuwa ga Ubangiji, raɓawa ta haƙiƙa sai ta gasgata ɗaiɗaikun waɗannan sunayen kuma suka ɗaukaka da wannan jerin, sai wannan falalar ta tabbata garesu. Waninsa kuma ya ce: Hikima a cikin taƙaituwa akan sunaye biyu cewa a cikin Alƙur'ani raɓa bawa zuwa wani suna daga cikn sunayen Allah - Maɗƙaukakin sarki - bai afkuba banda biyun nan, Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: {Lallai cewa shi yayin da bawan Allah ya tsaya yana kiransa}, kuma Ya fada a cikin wata ayar daban: {Kuma bayin Ubangiji Arrahman}, kuma fadinSa - Madaukakin sarki - Yana karfafa shi: {Ka ce ku kira Allah ko ku kira Arrahman}.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1682) (2132). فتح الباري لابن حجر (10/ 570).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com