Duniya jin daɗi ce, fiyayyen jin daɗin duniya shi ne mace ta gari
عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَخَيْرُ مَتَاعِ الدُّنْيَا الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ».
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Duniya jin daɗi ce, fiyayyen jin daɗin duniya shi ne mace ta gari.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin cewa ita duniya da abin da ke cikinta wani abu ne da za a ji dadi da shi, na wani lokaci sannan ya wuce, to, mafificin jin daɗinta shi ne mace ta gari, wacce idan ya kallaceta za ta faranta masa, idan kuma ya umarceta za ta yi masa biyayya, idan ba ya nan za ta tsare shi a kanta da kuma dukiyarsa.
Fa’idoji
Halaccin jin daɗi da abubuwa na halak a duniya wanda Allah Ya halatta wa bayinSa ba tare da ɓarna ko gadara ba.
Kwaɗaitarwa a kan zaɓin mace ta kwarai, domin taimako ce ga mijinta wajen biyayya ga Ubangijinsa.
Mafificin jin daɗin duniya shi ne abin da ya kasance a kan bin Allah, ko ya taimaka a kan hakan.
Madogara
صحيح مسلم (2/ 1090) (1467).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 365).
كشف المشكل من حديث الصحيحين، لابن الجوزي (4/ 129).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخن وغيره (1/ 286).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com