Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SHAYARWA

Hadisai 3

Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa

عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الرَّضَاعَةُ تُحَرِّمُ مَا تُحَرِّمُ الوِلَادَةُ».
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: «Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abin da haihuwa da nasaba suke haramtawa na yakumbo (Inna) ce ko baffa ko ɗan uwa...to shayarwa tana haramta shi, kuma shayarwa tana halatta abin da haihuwa take halattawa na hukunce-hukunce.

Fa’idoji
  1. Hadisin ƙa'idace a cikin huknce-hukuncen shayarwa.
  2. Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Shayarwa tana haramta abin da haihuwa take haramtawa) wato: Kuma tana halatta abin da take halattawa, shi ne a ijma'i a kan abin da yake rataye da haramcin aure da abubuwan da ke biye da shi, da yaɗuwar haramci tsakanin wanda aka shayar da kuma 'ya'yan mai shayarwar, da saukar da su a matsayin 'yan'uwa a cikin halaccin kallo da kaɗaitaka da tafiya. Saidai ragowar hukunce-hukunen 'yan uwantaka ba ya hawa a kansa na gado tsakani da wajabcin ciyarwa da 'yantawa ta hanyar mallaka da shaida da diyya da kuma sarayar da ƙisasi.
  3. Tabbatar da hukuncin haramci na har abada ta hanyar shayarwa.
  4. Wasu hadisan daban, sun yi nuni akan cewa haramci ta hanyar shayarwa yana tabbata ne da shayarwa biyar sanannu, kuma su zama a cikin shekara biyun farko (na wanda aka shayar ɗin).
  5. Waɗanda suka haramta ta hanyar nasaba su ne: Iyaye mata, kakanni mata suna shiga ciki, ko da kakannin kakanni ne ta ɓangaren uwa da uba. Da 'ya'ya mata: 'Ya'yan 'ya'ya mata suna shiga ciki, da 'ya'yan 'ya'ya ko sunyi nisa. Da 'yan uwa mata: Duk ɗaya ne shin sun kasance ta ɓangaren uba da uwa ne, ko ta ɓangaren ɗayansu. Da baffannai: Kuma dukkanin 'yan uwan uba shaƙiƙai da waɗanda ba shaƙiƙaiba suna shiga ciki, haka nan dukkanin 'yan uwan kakanninka, ko da sun yi nisa. Da yakumbai: Kuma dukkanin 'yan uwan uwa shaƙiƙai da wasunsu suna shiga ciki, haka nan dukkanin 'yan uwan kakanni, ko da sun yi nisa, duk ɗaya ne shin sun kasance ne kakanni ta ɓangaren uba ko ta ɓangaren uwa, da 'ya'yan ɗan uwa, da 'ya'yan 'yar uwa, da 'ya'yansu suna shiga cikinsu ko da sun yi nisa.
  6. Waɗanda suka haramta da shayarwa, dan haka duk abin da yake haramta saboda nasaba to yana haramta saboda shayarwa, duk matar da ta haramta saboda nasaba to kwatankwacinta ta haramta saboda shayarwa, sai uwar ɗan uwansa da 'yar uwar ɗansa daga shayarwa to bata haramta.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 170) (2646). صحيح مسلم (2/ 1068) (1444). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص96). الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله المحسن (ص84).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Daga Abdullahi Dan Abbas-Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah-tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce game da 'Diyar Hamza: "Bata halatta a gare ni ba, domin shayarwa ta haramta abin da nasaba take haramtawa, kuma ita Diyar Dan uwana na shayarwa ne

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم في بنت حمزة: «لَا تَحِلُّ لِي يَحْرُمُ من الرَّضَاعِ مَا يَحْرُمُ من النَّسَبِ وهي ابنة أَخِي من الرَّضاعة».
Daga Abdullahi Dan Abbas-Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah-tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce game da 'Diyar Hamza: "Bata halatta a gare ni ba, domin shayarwa ta haramta abin da nasaba take haramtawa, kuma ita Diyar Dan uwana na shayarwa ne
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aliyu Dan Abu Dalib-Allah ya yarda da shi- daga Annabi cewa ya Auri 'Diyar Baffansa Hamza. sai ya bashi labari cewa bata halatta a gareshi ba, domin ita 'Diyar Dan uwansa ce da aka shayar da su tare, kuma cewa shi da Baffan sa dukkansu Suwaiba ta shayar da su kuma baiwa ce ta Abu Laha, sai ya zamanto Dan uwansa ta wajen Shayarwa, kuma ya zamanto Baffan 'Diyarsa, kuma ya haramta ta hanyar shayarwa, duk abunda haihuwa ta haramta.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381ه. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com