Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

IDDA

Hadisai 3

Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan akurkin Da ki, kuma tasanya Mafi mufi daga cikin kayanta kuma babu ruwanta da Turare ko wani abun Ado har sai ta cika shekar, sannan sai azo da wata Dabba-Jaki ne ko Tsuntsu ko Akuya- sai fansheta da shi.

عن أم سلمة رضي الله عنها مرفوعاً: «جاءت امرأة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: يا رسول الله، إن ابنتي توفي عنها زوجها، وقد اشتكت عينها أفَنَكْحُلُها؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : لا -مرتين، أو ثلاثا-، ثم قال: إنما هي أربعة أشهر وعشر، وقد كانت إحداكن في الجاهلية ترمي بالبَعْرَةِ على رأس الحول». فقالت زينب: كانت المرأة إذا توفي عنها زوجها: دخلت حفشا، ولبست شر ثيابها، ولم تَمَسَّ طيبا ولا شيئا حتى تمر بها سنة، ثم تؤتى بدابة -حمار أو طير أو شاة- فتَفْتَضُّ به! فقلما تفتض بشيء إلا مات! ثم تخرج فتُعطى بعرة؛ فترمي بها، ثم تراجع بعد ما شاءت من طيب أو غيره».
Daga Ummu Salama-Allah ya yarda da ita- daga Annabi: "Wata Mata tazo wajen Manzon Allah sai ta ce: Ya Manzon ALlah, Lallai cewa 'Diyata Mijinta ya mutu ya barta, kuma ga shi tana fama da ciwon Ido shin ta iya sanya Kwalli? sai ya ce: AA Sau biyu ko Sau Uku sannan ya ce: "Ai ita (Iddar Mutuwa) iya Wata Hudu da kwana goma, kuma dayarku ta kasance a lokacin Jahiliyya ana jifanta da kashin Dabbobi har tsawon Shekara" Sai Zainab ta ce: Mata sun kasance idan Mijinta ya Mutu: sai ta shiga Dan akurkin Da ki, kuma tasanya Mafi mufi daga cikin kayanta kuma babu ruwanta da Turare ko wani abun Ado har sai ta cika shekar, sannan sai azo da wata Dabba-Jaki ne ko Tsuntsu ko Akuya- sai fansheta da shi, kuma da wuya a iya fansar ta ma da wani face sai ya mutu, sannan ta futo sannan sai abata kashin Rakumi; sai tayi jifa da shi, sannan ta dawo da sa turaren da duk abinda ta so
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Musulunci ya zo, kuma ka gusarwa Mutane dukkan kazantar Jahiyya, Musamman ma ga Mata, domin suna munana Mu'amala ga Matan kuma suna Zaluntarta, Sai Musulunci ya kwato mata hakkinta, to a cikin wannan Hadisin wata Mata ta zo tana neman fatawar Annabi cewa Mijin Diyarta ya Mutu, kuma zata yi masa Iddakuma Mai Idda bata Kwalliya, saidai kuma tana fama da ciwon Ido, shin anyi mata rangwame da ta yi amfani da Kwalli ne? sai Annabi ya ce Mata AA kuma yana mai maimaita mata hakan, sannan ya karanta mata ganin tsawon muddar Iddar tata, wanda Mace zata yi Idda ne fa don Alfarmar Mijinta tsawon wata hudu da kwana goma, yanzu ba zata iya jurewa ba a wanna Dan lokacin kadan wanda ba shi da wani tsawo? kuma Mata sun kasance a Jahiliyya, suna shiga Idda ne cikin Dan wani karamin Daki kamaer wani ramin kura, kuma su daina kwalliya, da saka turare, haka ma yin amfani da ruwa, da kuma cudanya da Mutane, sai Mace tayi cidin cidin da Dauda da kazanta na rashin wanka, kuma ba ita babu Mutane, shekara guda cur, to idan ta gama gama iddar sai a bata kashin Rakumi tayi jifa da shi, wannan shi yake nuna cewa duk wannan wahalar da ta shiga babu wani abu na kimantawa da ta yi na wannan abu da tayi don Mijinta sai wannan wulakantaccen abun (KashinRakumi) sa i Musulunci ya zo ya canza Mata waccan wahala da wata Ni'ama, da kuma wancan tsananin, kuma Sannan yaya ba zata iya hakuri ba da kwallin Idonta, to don haka babu Rangwame a gareta, don kada hakan ya zama tsani izuwa bude kofar Ado ga Mai Takaba.

Madogara

- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه. الإعلام بفوائد عمدة الأحكام لابن الملقن المحقق: عبد العزيز بن أحمد بن محمد المشيقح دار العاصمة للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية الطبعة: الأولى، 1417 هـ - 1997 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma

عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضيَ اللهُ عنها أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا تُحِدُّ امْرَأَةٌ عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ ثَلَاثٍ إِلَّا عَلَى زَوْجٍ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا، وَلَا تَلْبَسُ ثَوْبًا مَصْبُوغًا إِلَّا ثَوْبَ عَصْبٍ، وَلَا تَكْتَحِلُ، وَلَا تَمَسُّ طِيبًا إِلَّا إِذَا طَهُرَتْ نُبْذَةً مِنْ قُسْطٍ أَوْ أَظْفَارٍ».
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma, kuma kada ta sanya tufa rinanniya sai tufa na asb (wasu tufafi ne na Yaman masu fari da baƙi), kuma kada ta sa kwalli, kuma kada ta shafa tirare sai dai idan ta yi tsarki sai ta shafa wani gutsire na tiraren ƙusɗ ko azfar».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani ga mai idda (takaba) daga barin ado na tirare da kwalli da kayan ado da kyawawan kayan sawa ga mamaci sama da kwana uku, uba ne ko ɗan'uwa ko ɗa ko wasunsu, sai ga miji kawai wata huɗu da kwana goma, kuma alokacin iddarta (takaba) ga miji, kar ta sanya dukkanin rinannun tufafi dan yin ado sai tufafin asb, shi ne tufa na Yaman wanda ake rinawa kafin a saƙa shi, kuma kada ta sa kwalli a ido dan yin ado, kada ta shafa tirare mai ƙanshi da waninsu, sai dai idan ta yi wankan haila, sai ta shafa wani gutsire ƙarami na tiraren ƙusɗ ko azafar, su wasu nau’uka ne sanannu na tiraren wuta, basu zama daga manufar shafa tirare ba, an yi rangwami a cikinsa ga wacce ta yi wankan daukewar al’ada dan kawar da warin da ba'a so, da zata bibiyi gurbin jini da shi a acikin farji ba dan shafa tirare ba.

Fa’idoji
  1. Ma'anar idda (takaba) shi ita ce: Barin ado da abinda yake jan hankali zuwa ga aurenta, to yana wajaba akanta ta nisanci dukkanin kayan ado, da dukkanin tirare, da kwalli, kuma ta nisanci tufafin ado.
  2. Hani daga takabar mace ga mamaci sama da kwana uku, banda mijinta.
  3. Bayanin matsayin miji, dan ba'a yin idda ga waninsa sama da darare uku.
  4. Halaccin kwana uku ko ƙasa da haka, dan yaye baƙin cikin dake cikin rai.
  5. Wajabcin takabar mace ga mijinta wata huɗu da kwana goma, muddin dai bata zama mai ciki ba to iddarta shi ne idan ta haife ɗan dake cikin ciki.
  6. An halatta mata rinannen tufa idan ba na ado ba ne, amma abin lura a sanin haka shi ne a al'adance.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 60) (5342- 5343). صحيح مسلم (2/ 1127) (938). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 81). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص608).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Bai halatta ga Mace ba tayi Imani da Allah da kuma ranar lahira tayi Takabar mutuwa sama da da uku, sai dai in akan Miji ne: Wata hudu da kwana goma

عن زينب بنت أبي سلمة قالت: تُوُفِّيَ حَمِيْمٌ لأم حبيبة، فدعت بصُفْرَةٍ، فَمَسحَتْ بذراعيها، فقالت: إنما أصنع هذا؛ لأني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «لا يحل لامرأة تؤمن بالله واليوم الآخر أن تُحِدَّ على ميت فوق ثلاث، إلا على زوج: أربعة أشهر وعشرًا».
Hamim ya Mutu ya bar Ummu Habiba sai tasa aka kawo mata wani abu mai rawaya, sai ta shafe hannunta, sai tace: cewa nayi wannan ne; domin naji Annabi yana cewa: "Bai halatta ga Mace ba tayi Imani da Allah da kuma ranar lahira tayi Takabar mutuwa sama da da uku, sai dai in akan Miji ne: Wata hudu da kwana goma"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Mahaifin Ummu Habiba ya rasu, kuma ta kasance taji hanin yin takaba sama da Uku sai akan miji, sai ta so tabbatar da aiki da wannan Hadisi, sai ta nemi akawo mata turare wanda yake an cudanya shi da wani abu rawaya, sai ta shafi dantsenta, kuma tayi bayanin abinda ya sanya ta ta saka Turaren kuma shi cewa ita taji Annabi yana cewa: "Bai halatta ga Mace ba tayi Imani da Allah da kuma ranar lahira tayi Takabar mutuwa sama da da uku, sai dai in akan Miji ne: Wata hudu da kwana gom"

Madogara

- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه. - خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام- فيصل بن عبد العزيز بن فيصل ابن حمد المبارك الحريملي النجدي - الطبعة: الثانية، 1412 هـ - 1992 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com