Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

MASU CINYE SAURA

Hadisai 1

Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abotansu, abin da ya rage to namiji makusanci shi ne ya fi cancantarsa

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أَلْحِقُوا الفَرَائِضَ بِأَهْلِهَا، فَمَا بَقِيَ فَلِأَوْلَى رَجُلٍ ذَكَرٍ».
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abotansu, abin da ya rage to namiji makusanci shi ne ya fi cancantarsa ».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya umarci masu raba gado da su raba wa waɗanda suka cancanci rabon bisa adalci kamar yadda sharia ta yi bayani, kamar yadda Allah Yake nufi, sai a baiwa magada abin da Allah ya kaddarawa kowa a cikin Littafinsa, shi ne biyu cikin uku, da ɗaya cikin uku, da ɗaya cikin shida, da Rabi, da ɗaya cikin huɗu, da ɗaya cikin takwas. Abin da ya yi saura bayan wannan, to sai a baiwa mafi kusanci ga mamacin daga cikin maza; su ake kira Asubai.

Fa’idoji
  1. Hadisin ƙa'ida ce a cikin rabon gado (dukiyar da mamaci ya bari).
  2. raba gado yana farawa ne ta hanyar farawa da masu ci da lamba .
  3. Abin da ya rage bayan ci da farilla to sai abaiwa asibai.
  4. Gabatar da mafi kusanci sannan mafi kusanci, dan haka asibi ba ya gado kamar baffa tare da samun asibin da ya fi shi kusanci kamar uba.
  5. Babu komai ga asibi idan ci da lamba ya ƙarar da dukkanin dukiyar da mamaci ya mutu ya bari, wato bai bar komai ba daga cikinsu.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 152) (6737). صحيح مسلم (3/ 1233 - 1234) (1615). فتح الباري، لابن حجر (12/ 28). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 53). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص554). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص276).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com