Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

RANTSUWA DA BAKANCE

Hadisai 16

Sa'ad Dan Ubada ya yi wa MAanzon Allah fatawa game da alwashi da mahaifiyarsa ta yi, wanda hara ta murtu bata cika shi ba? , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah yace: sai ka yi mata

عن عَبْدُ الله بْنُ عَبَّاسٍ رضي الله عنه قال: «استَفْتَى سعد بن عُبَادَةَ رسول الله في نَذْرٍ كان على أمِّه، تُوُفِّيَتْ قبل أَنْ تقضيَهُ، قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : فاقْضِهِ عنها».
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- yace: Sa'ad Dan Ubada ya yi wa Manzon Allah fatawa game da alwashi da mahaifiyarsa tayi, wanda har ta mutu bata cika shi ba?, sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: sai ka yi mata
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ummu Saad ta rasu bata cika wani alwashi da ke kanta ba, sai Annabi tsira da amincin Allah ya umarci Danta da ya yii mata

Madogara

صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ نَهَى عَنِ النَّذْرِ، وَقَالَ: «إِنَّهُ لَا يَأْتِي بِخَيْرٍ، وَإِنَّمَا يُسْتَخْرَجُ بِهِ مِنَ الْبَخِيلِ».
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Shi ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga bakance, shi ne mutum ya wajabtawa kansa wani abu wanda shari'a ba ta wajabta masa ba, kuma ya ce: Lallai bakance ba ya gabatar da komai kuma ba ya jinkirtar da shi, kawai ana fitar da shi ne daga marowacin da ba ya aikata komai sai wajibin da ke kansa kawai, kuma bakance ba ya zuwa da abinda ba'a kaddara masa shi ba.

Fa’idoji
  1. Ba'a shara'anta bakance ba, sai dai idan ya yi bakance to cika shi ya wajaba idan ba sabo ba ne.
  2. Sababi a hanin (cewa shi ba ya zuwa da alheri); domin ba ya juyar da komai daga hukuncin Allah; kuma kada mai bakancen ya yi zatan cewa samun abinda yake nema ya kasance ne da sababin bakancen, Allah - Maɗaukakin sarki - Mawadaci ne daga hakan.
  3. Kurɗubi ya ce: Wannan hanin bigiransa misali ya ce: Idan Allah Ya warkar da mara lafiya na to na wajabta wa kaina kaza. Ta yadda karhancin yake shi : yayin da ya tsayar da aikin kusanci akan faruwar abinda yake so, ya bayyana cewa shi niyyar neman kusanci ga Allah - Maɗaukakin sarki - ba ta zama tsantsa ba saboda abinda ya bijiro da shi, kai ya shiga hanyar neman canji, kuma ya bayyanar da shi cewa shi da bai warkar da mara lafiyansa ba, da bai yi sadaka da abinda ya rataya akan warkar da shi ba, wannan shi ne halin marowaci, cewa shi ba ya fitar da wani abu daga dukiyarsa sai da wani canji magaggauci da zai yi kari kan abinda ya fitar a galibi.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 124) (6608). صحيح مسلم (3/ 1261) (1639). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص353). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص693).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin

عَنْ أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: أَتَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي رَهْطٍ مِنَ الأَشْعَرِيِّينَ أَسْتَحْمِلُهُ، فَقَالَ: «وَاللَّهِ لاَ أَحْمِلُكُمْ، مَا عِنْدِي مَا أَحْمِلُكُمْ» ثُمَّ لَبِثْنَا مَا شَاءَ اللَّهُ فَأُتِيَ بِإِبِلٍ، فَأَمَرَ لَنَا بِثَلاَثَةِ ذَوْدٍ، فَلَمَّا انْطَلَقْنَا قَالَ بَعْضُنَا لِبَعْضٍ: لاَ يُبَارِكُ اللَّهُ لَنَا، أَتَيْنَا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَسْتَحْمِلُهُ فَحَلَفَ أَنْ لاَ يَحْمِلَنَا فَحَمَلَنَا، فَقَالَ أَبُو مُوسَى: فَأَتَيْنَا النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَذَكَرْنَا ذَلِكَ لَهُ، فَقَالَ: «مَا أَنَا حَمَلْتُكُمْ، بَلِ اللَّهُ حَمَلَكُمْ، إِنِّي وَاللَّهِ -إِنْ شَاءَ اللَّهُ- لا أَحْلِفُ عَلَى يَمِينٍ، فَأَرَى غَيْرَهَا خَيْرًا مِنْهَا، إِلَّا كَفَّرْتُ عَنْ يَمِينِي، وَأَتَيْتُ الَّذِي هُوَ خَيْرٌ».
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mutane daga Ash'arawa ina neman ya dauki nauyinmu, sai ya ce: "Wallahi ba zan dauki nauyinku ba, bani da abinda zan dauki nauyinku" Sannan muka zauna lokacin da Allah Ya so, sai aka zo da wasu rakuma, sai ya yi mana umarni da rakuma uku, lokacin da muka tafi sai sashinmu suka ce da sashi: Allah ba Zai yi mana albarka ba, mun zowa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muna neman ya dauki nauyinmu sai ya yi rantsuwa cewa ba zai dauki nauyinmu ba sai kuma ya dauki nauyinmu, sai Abu Musa ya ce: sai muka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai muka ambata masa hakan, sai ya ce: "Ba nine na ɗauki nauyinku ba, a’a Allah ne Ya ɗauki nauyinku, Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Musa Al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da shi akwai wasu jama'a daga kabilarsa, manufarsu ita ce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya basu rakuman da zasu hau; dan samun damar fita yaki, sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyin su ba, ba shi da abinda zai dauki nauyinsu da shi, sai suka koma suka zauna tsawon wani lokaci, sannan wasu rakuma uku suka zo wa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, sai ya aika musu, sai sashinsu ya cewa sashi: Allah ba zai yi mana albarka a wadannan rakuma ukun ba; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyinmu ba, sai suka zo masa suka tambaye shi , sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Wanda ya dauki nauyinku Shi ne Allah - Madaukkain sarki -; domin cewa Shi ne Mai datarwa kuma Mai azirtawa, kadai ni sababi ne wanda hakan ya gudana ta hannuna, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na rantse da Allah, idan Allah Ya so ba na rantsuwa akan wani abu da aikata shi ko na bar shi, kuma in ga wanin wannan abinda na rantse akansa shi ne mafi alheri, sai na aikata abinda yafin kuma in bar wanda na rantse akansa din, kuma in yi kaffarar rantsuwa ta.

Fa’idoji
  1. Halaccin rantsuwa ba tare da ansa a yi rantsuwa ba; dan karfafa labari koda ya kasance a nan gaba ne.
  2. Halaccin togaciya da fadinsa: In Allah Ya so", bayan rantsuwa, kuma togaciya idan an yi niyya tare da rantsuwa, kuma hakan ya kasance a hade da rantsuwar to kaffara bata wajaba akan wanda ya yi karya rantsuwarsa.
  3. Kwadaitarwa a kan sabawa rantsuwa idan ya ga waninta shi ne mafi alheri daga rantsuwar, kuma ya yi kaffarar rantsuwarsa.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 146) (6718). صحيح مسلم (3/ 1268) (1649). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص345). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص682).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Sulaiman Xan Dauda -Amincin Allah a gare shi ya ce: "Na rantse a wannan Daren zan taki Matana guda Saba'in kowace mace daga cikin su zata haifi Yaron da zaiyi jahadi a Tafarkin Allah

عن أبي هُريرة رضي الله عنه عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم قال: "قال سليمان بن داود -عليهما السلام-: لَأَطُوفنَّ الليلةَ على سَبْعينَ امرأةً، تَلِدُ كلُّ امرأةٍ منهن غُلامًا يقاتلُ في سبيلِ الله، فقِيل له: قل: إن شاءَ الله، فلم يَقُلْ، فطافَ بهنَّ، فلم تَلِدْ منهن إلا امرأةٌ واحدةٌ نصفَ إنسانٍ". قال: فقال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم : "لو قالَ: إن شاء الله لم يَحْنَثْ، وكان دَرَكًا لحاجتهِ".
Daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah SAW ya ce: "Sulaiman Xan Dauda -Amincin Allah a gare shi ya ce: "Na rantse a wannan Daren zan taki Matana guda Saba'in kowace mace daga cikin su zata haifi Yaron da zaiyi jahadi a Tafarkin Allah
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

-صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. -صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ. -عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. -تأسيس الأحكام، للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414ه. -تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. -الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط. دار الفكر بدمشق، الطبعة الأولى 1381هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ka riqe wani vangaren na dukiyarka yafi maka Al-kairi

عن كَعْب بن مالك رضي الله عنه قال: قلتُ: يا رسولَ الله، إن مِن تَوبتي أن أَنْخَلِعَ مِنْ مالي؛ صدقةً إلى الله وإلى رسولِه، فقال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم : "أمسِكْ عليك بعضَ مالِكَ؛ فهو خيرٌ لكَ".
Daga Ka'ab Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya ce: na ce: ya manzon Allah lallai ne daga cikin tuba na in rabu da dukkan Dukiya ta; Sadaka saboda Allah da Manzon sa, sai manzon Allah SAW ya ce: "Ka riqe wani vangaren na dukiyarka yafi maka Al-kairi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

-صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه. -صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ. -عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. -تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414ه. -تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. -الإلمام بشرح عمدة الأحكام, إسماعيل الأنصاري, الطبعة الثانية 1392هـ. -الشرح الممتع على زاد المستقنع، محمد بن صالح بن محمد العثيمين، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى، 1422- 1428هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَلَفَ عَلَى يَمِينٍ وَهُوَ فِيهَا فَاجِرٌ لِيَقْتَطِعَ بِهَا مَالَ امْرِئٍ مُسْلِمٍ، لَقِيَ اللَّهَ وَهُوَ عَلَيْهِ غَضْبَانُ». قَالَ: فَقَالَ الْأَشْعَثُ: فِيَّ وَاللَّهِ كَانَ ذَلِكَ؛ كَانَ بَيْنِي وَبَيْنَ رَجُلٍ مِنَ الْيَهُودِ أَرْضٌ، فَجَحَدَنِي، فَقَدَّمْتُهُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلَكَ بَيِّنَةٌ؟» قُلْتُ: لَا. قَالَ: فَقَالَ لِلْيَهُودِيِّ: «احْلِفْ». قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِذَنْ يَحْلِفَ وَيَذْهَبَ بِمَالِي. فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: {إِنَّ الَّذِينَ يَشْتَرُونَ بِعَهْدِ اللَّهِ وَأَيْمَانِهِمْ ثَمَنًا قَلِيلًا}. إِلَى آخِرِ الْآيَةِ.
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa". ya ce: Sai Ash'As ya ce: Wallahi a kaina hakan ya kasance; ya kasance akwai wani fili tsakanina da wani mutum cikin Yahudawa, sai ya yi min musun filin, sai na kawo shi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce dani: "Shin kana da shaidu?" Na ce: A'a. Ya ce: Sai ya cewa Bayaahudan: "Ka rantse". Ya ce: Na ce: Ya manzon Allah, to sai ya rantse ya tafi da dukiyata. Sai Allah - Maɗaukin sarki - ya ce: {Lallai ne wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani farashi dan kadan}. har zuwa ƙarshen ayar,
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga yin rantsuwa tare da sanin mai rantsuwar cewa shi maƙaryaci ne a cikinta, dan ya ya karbi dukiyar waninsa; to zai gamu da Allah alhali Yana mai fushi da shi. Sai Ash'As ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa , Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi hakan lokacin da ya kasance akwai rigima ta mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum cikin Yahudawa, sai suka kai ƙara zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya cewa Ash'As: Wajibi ne ka zo da shaidun da suke tabbatar da abinda kake ƙararsa, idan ka kasa to baka da wani abu sai rantsuwar abokin rigimarka wanda ake ƙararsa, sai al-Ash'As ya ce: Ya manzon Allah, to bayahude zai rantse kuma ba ya taka tsantsan ya tafi da dukiya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da gasgata hakan a cikin Alƙur'ani a faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Lallai waɗanda suke musanya}. Suke canja {da alƙawarin Allah}, da wasiyyarSa ga muminai da dawo da amana {da rantse-rantsensu} da rantsuwarsu da sunanSa suna maƙaryata {ɗan kudi kaɗan} na rabon duniya {To waɗannan basu da wani rabo a lahira} kuma basu da wani nasibi {Kuma Allah ba Zai yi musu magana ba}, da zancen da zai faranta musu rai ya amfanar da su ba, kai ya yi fushi da su, {Kuma ba Zai kallesu ba a ranar alƙiyama} kallo na rahama da kyautatawa, {Kuma ba Zai tsarkakesu ba} da yabo mai kyau ba, kuma ba Zai tsarkakesu da gafara daga zunubai da datti ba {Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a garesu} mai sa ciwo saboda abinda suka aikata.

Fa’idoji
  1. Hani daga halatta dukiyoyin mutane da ƙarya.
  2. Kaurara haƙƙoƙin musulmai a ƙanƙanin haƙƙi da mai yawansa.
  3. Shaidu suna kan mai kawo ƙara, rantsuwa kuma tana kan wanda aka kai ƙara idan ya musa.
  4. Tabbatar da haƙƙi da shaidu biyu, idan ba’a samu shaidu a wurin mai ƙara ba, to rantsuwa ta wajaba akan wanda aka kai ƙara.
  5. Haramta rantsuwa (mai dulmiyarwa) ita ce ta ƙarya wacce mai rantsuwa yake ƙwace haƙƙin waninsa da ita, kuma ita tana daga cikin manyan zunubai, wacce take bijirar da mai ita ga fushin Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma uƙubarSa.
  6. Shugaba ya yi wa abokanan rigima wa'azi, musamman ma a lokacin nufin yin rantsuwa.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 121) (2416). صحيح مسلم (1/ 123) (138). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 136). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص687). فتاوى اللجنة الدائمة - اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء (23/ 513).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk wanda ya rantse kan wata rantsuwada ya takure kansa da ita yana son karvar Dukiyar wani Musulmi, kuma a halin Qarya ya ke, zai gamu da Allah SWT yana fushi da shi

عن عبد الله بن مسعودٍ رضي الله عنه مرفوعًا: (من حلف على يَمِينِ صَبْرٍ يَقْتَطِعُ بها مال امرئ مسلم، هو فيها فاجر، لقي الله وهو عليه غضبان)، ونزلت: (إن الذين يشترون بعهد الله وأيمانهم ثمنا قليلا) إلى آخر الآية".
Duk wanda ya rantse kan wata rantsuwada ya takure kansa da ita yana son karvar Dukiyar wani Musulmi, kuma a halin Qarya ya ke, zai gamu da Allah SWT yana fushi da shi
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. - صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. - تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، القاهرة، الطبعة: الأولى 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yar uawata tayi bakancen zata je dakin Allah babu Takalmi, sai ta \umarce ni da na tambayi Manzon Allah SAW sai na tambaye shi, sai ya ce: ta tafi kuma tana iya hawan abin hawa

عن عُقْبَة بْن عَامِرٍ رضي الله عنه قال: «نَذَرَتْ أُخْتِي أَنْ تَمْشِيَ إلَى بَيْتِ الله الْحَرَامِ حَافِيَةً، فَأَمَرَتْنِي أَنْ أَسْتَفْتِيَ لَهَا رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم فَاسْتَفْتَيْتُهُ، فَقَالَ: لِتَمْشِ وَلْتَرْكَبْ».
Daga Ukuba Bn Amir -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Yar \uawata tayi bakancen zata je dakin Allah babu Takalmi, sai ta \umarce ni da na tambayi Manzon Allah SAW sai na tambaye shi, sai ya ce: ta tafi kuma tana iya hawan abin hawa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Daga dabi'ar Dan Adam da yake gaggutawa wani lokaci, don haka ya zama tilas ya aikata abin da yake wahala ne a kansa, kuma shari'armu ta zo matsakaiciya, kuma ba ta da taurin rai a cikin ibada har sai ta ci gaba, kuma a cikin wannan hadisin Yar Uwar Uquba ta ne me shi da ya tambayii - Manzon Allah - cewa ta tayi bakancen zuwa harami mai alfarma ba tare da sanya takalmi ba, sai Annabi -SAW- ya gayawa wannan matar zata iya tafiya, don haka ya umurce ta da yin duk abin da za ta iya na tafiya, kuma ta hau abun hawa idan ba za ta iya tafiya ba.

Madogara

1- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. 2- صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. 3- خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز المبارك، الطبعة: الثانية 1412هـ، 1992م. 4- الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز، تحقيق: سعيد القحطاني، مؤسسة عبد العزيز بن باز الخيرية، الرياض، الطبعة: الأولى 1435هـ. 5- الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. 6- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، دار الميمان، الطبعة: الأولى 1426هـ، 2005م. 7- تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار المنهاج، الطبعة: 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 15
Hadisai 15
  1. Sa'ad Dan Ubada ya yi wa MAanzon Allah fatawa game da alwashi da mahaifiyarsa ta yi, wanda hara ta murtu bata cika shi ba? , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah yace: sai ka yi mata
  2. ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci
  3. Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin
  4. Sulaiman Xan Dauda -Amincin Allah a gare shi ya ce: "Na rantse a wannan Daren zan taki Matana guda Saba'in kowace mace daga cikin su zata haifi Yaron da zaiyi jahadi a Tafarkin Allah
  5. Ka riqe wani vangaren na dukiyarka yafi maka Al-kairi
  6. Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa
  7. Duk wanda ya rantse kan wata rantsuwada ya takure kansa da ita yana son karvar Dukiyar wani Musulmi, kuma a halin Qarya ya ke, zai gamu da Allah SWT yana fushi da shi
  8. Yar uawata tayi bakancen zata je dakin Allah babu Takalmi, sai ta \umarce ni da na tambayi Manzon Allah SAW sai na tambaye shi, sai ya ce: ta tafi kuma tana iya hawan abin hawa
  9. Ya kai Abdurrahman Dan Samra, Kada ka nemi Mulki, sabida Idan aka baka sabida kai ka nema to sai abarka da ita
  10. Wanda ya yi rantsuwa sannan ya ga cewa Allah yana jin tsoron ta, to sai taqawa ta zo
  11. Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare
  12. Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana
  13. Wanda ya rantse ya ce: Ni barrantacce ne daga Musulunci, kuma idan maƙaryaci ne, to ya kasance kamar yadda ya faɗa, kuma idan ya kasance mai gaskiya, to ba zai dawo Musulunci ba cikin kwanciyar hankali
  14. Annabi Isa xan Maryam yaga wani Mutum yana sata, sai ya ce da shi: Kayi sata? saiya ce: aa na rantse da Allah wada babu wani Ubangiji sai shi, sai Isa ya ce nayi Imani da Allah,kuma idona ya nunan Qarya
  15. Kaffarar bakance ita ce kaffarar rantsuwa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com