Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

"Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu"

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «للعبد المملوك المصلح أجران»، والذي نفس أبي هريرة بيده لولا الجهاد في سبيل الله والحج، وبر أمي، لأحببت أن أموت وأنا مملوك.
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu" kuma na rantse da wanda Ran Abuhuraira ya ke a Hannunsa ba don Jihadi a tafarkin Allah ba da kuma Hajji, da kuma biyayyar Mahaifiyata ba, da nai kwadayin na Mutu ina Bawa
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu"; saboda tsayuwa da hakkin Allah Madaukakin Sarki- na ibadu da tsayuwarsa da hakkin Maigidansa na Hidima, Sannan Abuhuraira -Allah ya yarda da shi- ya bada labarin cewa ba don babu Jahadi akan Bawa ba, da kuma tsayuwarsa ga Hidimar Mahaifiyarsa na ciyarwa da Hidima wallahi da na fi son in zamanto na Mutu a Matsayin yana Bawa sabida Ladan da yake cikinsa

Madogara

صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. صحيح مسلم, ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي, دار إحياء التراث العربي, بيروت. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشر, 1407ه. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لمحمد بن علان الصديقي, دار الكتاب العربي. كنوز رياض الصالحين، بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430ه. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي, دار ابن الجوزي. شرح رياض الصالحين لابن عثيمين، دار مدار الوطن للنشر، الرياض, الطبعة : 1426 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
BAYAR DA 'YANCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com