Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

WASIYYA

Hadisai 4

Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa

عَنْ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهُما أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا حَقُّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ لَهُ شَيْءٌ يُوصِي فِيهِ، يَبِيتُ ثَلَاثَ لَيَالٍ، إِلَّا وَوَصِيَّتُهُ عِنْدَهُ مَكْتُوبَةٌ»، قَالَ عَبْدُ اللهِ بْنُ عُمَرَ رضي الله عنهما: «مَا مَرَّتْ عَلَيَّ لَيْلَةٌ مُنْذُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ ذَلِكَ إِلَّا وَعِنْدِي وَصِيَّتِي».
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa", Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Wani dare bai taɓa wucewa gareni ba tunda na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗi haka ba sai wasiyyata tana tare da ni".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ba ya kamata ga wani musulmi da yake da wani abinda zai yi wasicci da shi na haƙƙoƙi ko dukiyoyi koda kaɗan ne, ya kwana darere uku, sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa. Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - Ya ce: Ban taɓa kwana a wani dare ba tunda na ji shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi haka sai wasiyyata tana tare da ni.

Fa’idoji
  1. Halaccin wasiyya da gaggawar yinta, dan yin bayani gareta, da kuma ruko da umarnin mai shara'antawa a cikinta, da yi wa mutuwa tanadi, da lura da ita da gurin bada ita, tun kafin wani abu mai shagaltarwa ya shagaltar da shi.
  2. Wasiyya: Ma'anarta, ita ce mutum ya alƙwarantawa wani mutum yin tasarrufin wani abu daga dukiyarsa bayan mutuwarsa, ko ya alƙawarantawa wani mutum kan ya kula da 'ya'yansa ƙanana, ko ya alƙawarantawa wani mutum a wani abu daga ayyukan da zai mallakesu bayan mutuwarsa.
  3. Wasiyya ta rabu gida uku: 1- Mustabbi, ita ce wasicci da wani abu daga dukiyarsa da za'a bada ita a tafarkin alheri, da kyautatawa; dan ladansa ya sadu da shi bayan mutuwarsa. 2- Ta wajibi, ita ce wasicci da abinda ke kansa na haƙƙoƙi, daidai ne sun kasance haƙƙoƙin Allah ne - Maɗaukaki sarki -, kamar zakkar da ba'a fitar da ita ba, ko kaffara, da makamancinsu daga abinda yake wajaba a asalin shari'a, ko waɗannan haƙƙoƙin sun kasance na 'yan Adam ne; kamar bashi, da maida amanoni. 3- wasiyyar da aka haramta, idan ta ƙaru akan sulusi (ɗaya bisa uku) daga dukiyarsa, ko idan ya yi wasicci ga wani mai gado.
  4. Falalar Ɗan Umar - Allah ya yarada da su -, da gaggawarsa zuwa aikata alheri, da bin Mai shara'antawa Mai hikima.
  5. Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Yin rangwami a cikin darare biyu ko uku dan kawar da ƙunci ne da kuma wahala.
  6. Abubuwa masu muhimmanci yana kamata a kiyayesu da yin rubutu; domin cewa hakan zai fi sasu tabbatuwa kuma zai fi sa wa a kiyaye haƙƙoƙi.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 2) (2738). صحيح مسلم (3/ 1250) (1627). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 48). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص548).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yazo min don ya dubani shekarar Hajjin ban-kwana daga wani ciwo da yayi tsanani agareni,sai nace:Ya Ma'aikin Allah,hakika ciwo yakai inda yakai agareni kamar yadda kake gani,kuma ni Ma'abocin Dukiya ne,bamai gadona sai 'ya mace bana yi Sadaka da Biyu bisa Ukun Dukiyata ba?yace:a'a,nace:Rabi fa ya Ma'aikin Allah?yace:a'a,nace:Daya bisa Ukufa?yace:Daya bisa Uku,kuma Daya bisa Uku da yawa,hakika cewa kai kabar Magadanka Mawadata shi yafi akan kabarsu Talakawa suna rokon Mutane,kuma cewa kai ba zaka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman Fuskar Allah face Allah ya baka lada da ita,hatta abinda zaka saka a Bakin Matarka.Yace:Nace ya Ma'aikin Allah zan barwa abokanaina a bayana?yace:Hakika cewa kai ba za'a barka ba ka aikata wani aiki da kake neman Fuskar Allah sai ka kara Daraja dashi da Daukaka,kuma watakila kuma idan aka barka har wasu su amfana da kai wasu kuma su cutu da kai,ya Allah ka cikawa Abokanaina Hijirarsu,kada ka juyar dasu a bayansu,sai dai sadauki shine Sa'ad Dan Khaula(yana yiwa Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-Rasa'i don ya Rasu a Makka)

عن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه قال: جاءني رسول الله صلى الله عليه وسلم يَعُودُنِي عام حَجَّةِ الوداع من وَجَعٍ اشْتَدَّ بي، فقلت: يا رسول الله، قد بلغ بي من الوَجَعِ ما ترى، وأنا ذو مال، ولا يَرِثُنِي إلا ابنةٌ أَفَأَتَصَدَّقُ بثلثي مالي؟ قال: لا، قلت: فالشَّطْرُ يا رسول الله؟ قال: لا، قلت: فالثلث؟ قال: الثلث، والثلث كثير، إنك إن تَذَرَ وَرَثَتَكَ أغنياء خيرٌ من أن تَذَرَهُم عالَةً يَتَكَفَّفُونَ الناس، وإنك لن تنفق نفقة تبتغي بها وجه الله إلا أُجِرْتَ بها، حتى ما تجعل في فِيْ امرأتك. قال: قلت: يا رسول الله أُخَلَّفُ بعد أصحابي؟ قال: إنك لن تُخَلَّفُ فتعمل عملا تبتغي به وجه الله إلا ازْدَدْتَ به درجة ورِفْعَةً، ولعلك أن تُخَلَّفَ حتى ينتفع بك أقوام، ويُضَرُّ بك آخرون. اللهم أَمْضِ لأصحابي هجرتهم، ولا تَرُدَّهُم على أَعْقَابِهِم، لكنِ البَائِسُ سعد بن خَوْلَةَ (يَرْثِي له رسول الله صلى الله عليه وسلم أن مات بمكة).
An karbo daga Sa'ad Dan Abi Wakkas-Allah ya yarda da shi-yace:Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yazo min don ya dubani shekarar Hajjin ban-kwana daga wani ciwo da yayi tsanani agareni,sai nace:Ya Ma'aikin Allah,hakika ciwo yakai inda yakai agareni kamar yadda kake gani,kuma ni Ma'abocin Dukiya ne,bamai gadona sai 'ya mace bana yi Sadaka da Biyu bisa Ukun Dukiyata ba?yace:a'a,nace:Rabi fa ya Ma'aikin Allah?yace:a'a,nace:Daya bisa Ukufa?yace:Daya bisa Uku,kuma Daya bisa Uku da yawa,hakika cewa kai kabar Magadanka Mawadata shi yafi akan kabarsu Talakawa suna rokon Mutane,kuma cewa kai ba zaka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman Fuskar Allah face Allah ya baka lada da ita,hatta abinda zaka saka a Bakin Matarka.Yace:Nace ya Ma'aikin Allah zan barwa abokanaina a bayana?yace:Hakika cewa kai ba za'a barka ba ka aikata wani aiki da kake neman Fuskar Allah sai ka kara Daraja dashi da Daukaka,kuma watakila kuma idan aka barka har wasu su amfana da kai wasu kuma su cutu da kai,ya Allah ka cikawa Abokanaina Hijirarsu,kada ka juyar dasu a bayansu,sai dai sadauki shine Sa'ad Dan Khaula(Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana yi masa Rasa'i don ya Rasu a Makka)
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sa'ad Dan Abi Wakkas Allah ya yarda dashi yayi rashin lafiya lokacin Hajjin ban kwana rashin lafiya maitsanani wacce saboda tsananinta yaji tsoran Mutuwa Sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya duba shi kamar yadda al'adarsa take cikin bibiyar Sahabansa da jajantawa a garesu Sai Sa'ad ya ambatawa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi damuwoyinsa, abinda ya kudira na cewa zai Sadaka da dukan Dukiyarsa, sai yace: Ya Ma'aikin Allah, hakika ciwo mai tsanani yayi tsanani agareni wanda nake jin tsoran Mutuwa daga gareshi, kuma ni ma'abocin Dukiya mai yawa ne, kuma cewa shi babu daga Magada Raunana wadanda nake tsoran talauci da tozarta a kansu face 'yata Guda daya, to bayan wannan shin na iya Sadaka da Biyu bisa Uku na Dukiyata, don na gabatar dashi ga managarcin aikina? sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace: a'a Yace: Rabi fa ya Ma'aikin Allah? yace: a'a yace: Daya bisa uku fa? sai yace: ba abinda zai hanaka Sadaka da Daya bisa uku duk da cewa mai yawa ne Domin cewa saukowa izuwa abinda yake koma bayansa na daga Daya bisa Hudu ko Daya bisa biyar shi yafi Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya bayyana masa Hikima cikin saukowa cikin Sadaka da mafi yawan Dukiya izuwa mafi karancinta da lamari Biyu: 1. shine cewa shi in ya mutu alhali ya bar Magadansa Mawadata masu amfani da Nagartarsa da Dukiyarsa to hakan shi yafi akan ya fitar dashi daga garesu izuwa waninsu, ya barsu suna rayuwa abisa kyautayin Mutane. 2. ko kuma a wanzar dashi ya sami Dukiyarsa, sai ya ciyar da ita ta hanyoyin da Shari'a ta shara'anta, kuma ya nemi lada awajan Allah sai a saka masa abisa hakan, har acikin abinda yake mafi wajabcin ciyarwa akansa shine abinda zai ciyar da Matarsa Sannan Sa'ad Dan Abi Wakkas yaji tsoran ya mutu a Maka wacce yayi Hijira daga gareta ya kuma barta saboda Allah Madaukaki, sai yin hakan ya tauye masa wani abu daga sakamakon Hijirarsa, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya bashi Labari cewa ba za'a barshi bisa dole a cikin Garin da yayi Hijira daga gareshi ba, sannan yayi wani aiki acikinsa don neman ladan Allah face ya kara Daraja da shi, sannan Annabi tsira da abincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Bushara da abinda yake nuni da cewa zai warke daga ciwonsa, Allah ya amfani Muminai dashi, ya kuma cutar da Kafirai dashi,sai hakan ta kasance kamar yadda Mai Gaskiya abin Gasgatawa ya bada labari, sai ya warke daga rashinlafiyarsa, kuma ya zama Jagora mafi Girma acikin yakin Farisawa, kuma Allah ya amfani Musulunci da Musulmai dashi, yayi Bude Bude kuma Allah ya cutar da Shirka da Mushirikai dashi, sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yiwa Sahabbansa Addu'a cewa ya tabbatar musu da Darajarsu, ya kuma karbeta daga garesu, kuma kada suyi Ridda a cikin Addininsu ko kuma kar ya mayar dasu Garin da suka yi Hijira daga gareshi, sai Allah ya karbi hakan daga gareshi, Godiya da Baiwa tasa ce, kuma dukkan Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya Daukaka Musulunci dasu Sannan ya ambaci Sa'ad Dan khaula,shi yana cikin masu kaura wadanda sukayi kaura daga Maka sai dai Allah ya kaddara cewa zai mutu acikinta, sai ya mutu kuwa acikin nata, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Rasa'i: ana nufin: bai ji masa dadi ba saboda ya mutu a Maka; hakika sun kasance suna ki ga wanda yayi Hijira ya mutu a Kasar da yayi Hijira daga gareta.

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام، للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية 1392هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام، تحقيق محمد صبحي حسن حلاق -مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426هـ. صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة، (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. المعجم الوسيط، نشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت – لبنان، الطبعة: الثانية.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Allah ya bawa dukkan Mai Haqqi Haqqinsa, kuma babu wata Wasiyya ga mai Gado, Kuma Xa na Ubansa ne, Kuma Karuwa za'a jefeta ne, Kuma duk wanda ya danganta Kansa zuwa Wanin Mahaifinsa ko Maulansa don yana qyamarsu to la'antar Allah ta tabbata a gare shi, Kuma Allah ba zai karvi wani aiki ko sadaka daga gare shi ba

عن عمرو بن خارجة رضي الله عنه : أن النبي صلى الله عليه وسلم خطب على ناقته وأنا تحت جِرَانِها وهي تَقْصَع بِجِرَّتِها، وإن لُعابها يَسِيل بين كتفيَّ فسمعتُه يقول: «إن الله أعطى كلِّ ذي حقٍّ حقَّه، ولا وصيَّةَ لِوارث، والولَد لِلْفِراش، وللعاهِرِ الحَجَر، ومن ادَّعى إلى غير أبِيهِ أو انْتمى إلى غير مَوَاليه رغبةً عنهم فعَلِيه لعنةُ الله، لا يَقْبَلُ الله منه صَرْفا ولا عَدْلا».
Allah ya bawa dukkan Mai Haqqi Haqqinsa, kuma babu wata Wasiyya ga mai Gado, Kuma Xa na Ubansa ne, Kuma Karuwa za'a jefeta ne, Kuma duk wanda ya danganta Kansa zuwa Wanin Mahaifinsa ko Maulansa don yana qyamarsu to la'antar Allah ta tabbata a gare shi, Kuma Allah ba zai karvi wani aiki ko sadaka daga gare shi ba
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

سنن الترمذي، تأليف: محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق أحمد شاكر وغيره، الناشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، الطبعة: الثانية، 1395 هـ سنن ابن ماجه, ابن ماجة أبو عبد الله محمد بن يزيد القزويني، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي, الناشر: دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي. مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. صحيح الجامع الصغير وزياداته, محمد ناصر الدين الأشقودري الألباني, الناشر: المكتب الإسلامي, , ط 3, 1408 هـ. الصحاح تاج اللغة وصحاح العربية, أبو نصر إسماعيل بن حماد الجوهري الفارابي, تحقيق: أحمد عبد الغفور عطار, دار العلم للملايين – بيروت, الطبعة: الرابعة 1407 هـ‍ - 1987 م. تاج العروس من جواهر القاموس, محمّد بن محمّد بن عبد الرزّاق الحسيني، أبو الفيض، الملقّب بمرتضى، الزَّبيدي, مجموعة من المحققين, الناشر: دار الهداية. معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م. معجم مقاييس اللغة، تأليف: أحمد بن فارس بن زكريا القزويني الرازي، تحقيق: عبد السلام محمد هارون، الناشر: دار الفكر عام النشر: 1399هـ - 1979م. شرح صحيح البخاري لابن بطال، تحقيق: أبي تميم ياسر بن إبراهيم، نشر: مكتبة الرشد، الرياض-السعودية، الطبعة: الثانية 1423ه، 2003م. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م. المصباح المنير في غريب الشرح الكبير, أحمد بن محمد بن علي الفيومي ثم الحموي، أبو العباس, المكتبة العلمية – بيروت. تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي, أبو العلا محمد عبد الرحمن بن عبد الرحيم المباركفورى, دار الكتب العلمية - بيروت. النهاية في غريب الحديث والأثر, مجد الدين أبو السعادات المبارك بن محمد الشيباني الجزري ابن الأثير, المكتبة العلمية - بيروت، 1399هـ - 1979م, تحقيق: طاهر أحمد الزاوى - محمود محمد الطناحي. شرح الطيبي على مشكاة المصابيح المسمى بـ (الكاشف عن حقائق السنن), شرف الدين الحسين بن عبد الله الطيبي, المحقق: د. عبد الحميد هنداوي, الناشر: مكتبة نزار مصطفى الباز (مكة المكرمة - الرياض), الطبعة: الأولى، 1417 هـ - 1997 م. بلوغ المرام من أدلة الأحكام، لابن حجر، دار القبس للنشر والتوزيع، الرياض - المملكة العربية السعودية، الطبعة: الأولى، 1435 هـ - 2014 م. فتاوى اللجنة الدائمة - المجموعة الأولى-: اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء- جمع وترتيب: أحمد بن عبد الرزاق الدويش. مجموع فتاوى العلامة عبد العزيز بن باز رحمه الله، أشرف على جمعه وطبعه: محمد بن سعد الشويعر- طبع وزارة الشؤون الإسلامية والأوقاف.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Maye ya xagaka ya kai Baban Huzaim?

عن حنظلة بن حِذْيَم، أن جدَّه حَنِيفَة قال لحِذْيَم: اجمع لي بنيَّ، فإني أريد أن أُوصِي، فجَمَعهم، فقال: إنَّ أوَّل ما أوصي أنَّ ليَتِيمي هذا الذي في حَجْري مائة من الإبل، التي كنا نُسمِّيها في الجاهلية: المُطَيِّبة، فقال حِذْيَم: يا أبَتِ، إني سمعت بَنِيك يقولون: إنما نُقِرُّ بهذا عند أَبِينا، فإذا مات رجَعْنا فيه، قال: فبَيْني وبيْنكم رسول الله صلى الله عليه وسلم ، فقال حِذيم: رَضِينا، فارْتَفَعَ حذيم، وحنيفة، وحنْظَلَة معهم غُلام، وهو رَدِيف لحذيم، فلما أتوا النبي صلى الله عليه وسلم ، سلَّموا عليه، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : «ما رَفَعَك يا أبا حذيم؟» قال: هذا، وضرَب بيده على فَخِذ حذيم، فقال: إني خَشِيتُ أن يَفْجَأَني الكِبَر، أو الموْت، فأردتُ أن أوصي، وإني قلتُ: إن أوَّل ما أوصي أن ليتيمي هذا الذي في حَجْري مائة من الإبل، كنا نُسَمِّيها في الجاهلية: المُطَيِّبة، فغَضِب رسول الله صلى الله عليه وسلم ، حتى رأَيْنا الغضب في وجهه، وكان قاعدًا فجَثَا على ركبتيه، وقال: «لا، لا، لا الصدقة خمس، وإلا فعشر، وإلا فخمس عشرة، وإلا فعشرون، وإلا فخمس وعشرون، وإلا فثلاثون، وإلا فخمس وثلاثون، فإن كَثُرت فأربعون» ، قال: فودَّعوه ومع اليتيم عصا، وهو يَضْرب جملا، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : «عَظُمَت هذه هراوة يتيم» ، قال حنظلة: فَدَنا بي إلى النبي صلى الله عليه وسلم ، فقال: إنَّ لي بَنِين ذوي لِحى، ودون ذلك، وإنَّ ذا أصغرُهم، فادع الله له، فَمَسَح رأسه، وقال: «بارك الله فيك» ، أو «بورك فيه» ، قال ذَيَّالٌ: فلقد رأيتُ حنظلة، يؤتى بالإنسان الوارِم وجهه، أو بالبهيمة الوارِمة الضَّرع، فيَتْفُل على يديه، ويقول: بسم الله، ويضع يده على رأسه، ويقول على موْضِع كف رسول الله صلى الله عليه وسلم ، فَيَمْسحه عليه، وقال ذيال: فَيَذْهب الوَرَم.
Daga Hanzala Bn Hizyam cewa Kakansa Hanifa ya ce: da Hizyam ka tara mun 'ya'ya na, saboda ina son inyi Wasiyya. sai ya tara su, sai ya ce: farkon abun da zanyi wasiyya shi ne cewa wannan Marayan nawa da yake kan cinyata in na mutu yana da Raqumi xari, wacce Muke kiranta a Jahiliyya Farantawa, sai Hizyam ya ce: ya Babana, naji 'Ya'yanka suna cewa: zamu yarda da wannan ne a gaban Babanmu idan ya Mutu ba zamu yarda ba, ya ce: to ai tsakanina da ku akwai Manzon Allah SAW, sai hizyam ya ce: Mun yarda sai Hizyam ya xaga da shi da Hanifa da Hanzala tare da su da yaron, kuma Hizyam ne ya goya shi a bayan abun Hawansa, yayin da suka isa wajen Manzon Allah SAW sai suka yi masa Sallama sai manzon Allah SAW ya ce: Mai ya taso ka ya Aba Hizyam? sai ya ce: wannan kuma sai ya daki cinyar hizyam da Hannunsa, sai ya ce: lallai ni ina jin tsoron kada tsufa ya cimmun ko kuma Mutuwa, shi yasa nake son nayi Wasiyya, kuma ni nace: cewa lallai farkon abunda zanyi Wasiyya da shi shi ne wannan Marayan nawada yake kan cinyata a bashi Raquma Xari, kuma muna kiranta a jahiliyya Kyautatawa, Sai Manzon Allah SAW yayi fushi har muka ga fushin a fuskarsa kuma yana Yana zaune sai ya durqusa kan Guiwoyinsa, kuma ya ce: A'a A'a Sadaqa Biyar ne, in kuma ba haka goma, in kuma ba haka ba to ashirin, in kuma ba haka ba Ashirin da Biyar in kuma ba haka ba Talatin in kuma ba haka ba Talatin da biyar idan kuma tayi yawa to arba'in" ya ce: sai suka yi masa bankwana da shi tare da Marayan akwai wani sanda, kuma da shi yake dukan Raqumin, sai Manzon Allah SAW ya ce: "Wanna sandar Mrayan tayi girma" Hanzala ya ce: sai ya kusanto dani zuwa Manzon Allah SAW sai ya ce: lallai ni ina da Yaya Maza ma'abota Gemu, da kuma qasa da haka kuma wannan shi ne Mafi qanqancinsu, ka roqa masa Allah, sai ya shafi kansa, kuma ya ce: "Allah yayi maka Al-barka" ko "An roqa maka Al-barka" Thayyal ya ce: kuma haqiqa naga Hanzala, ana zuwa da Mutum wanda fuskarsa ta kumbura ko dabba da Nononta ya kumbura sai yayi tofi a hannunsa kuma ya ce: da Sunan Allah sai ya sanya Hannunsa akan sa, kuma ya ce: akan wurin tafin Manzon Allah SAW sai ya shafeshi akai, kuma Thayyal ya ce: sai Kumburin ya tafi
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Hanzala Bn Hizyam bada labarin Kakansa Hanifa ya ce: da Hizyam ka tara mun 'ya'ya na, saboda ina son inyi Wasiyya. sai ya tara su, sai ya ce: farkon abun da zanyi wasiyya shi ne cewa wannan Marayan nawa da yake kan cinyata in na mutu yana da Raqumi xari, wacce Muke kiranta a Jahiliyya Farantawa, sai Hizyam ya ce: ya Babana, naji 'Ya'yanka suna cewa: zamu yarda da wannan ne a gaban Babanmu idan ya Mutu ba zamu yarda ba, ya ce: to ai tsakanina da ku akwai Manzon Allah SAW, sai hizyam ya ce: Mun yarda sai Hizyam ya xaga da shi da Hanifa da Hanzala tare da su da yaron, kuma Hizyam ne ya goya shi a bayan abun Hawansa, yayin da suka isa wajen Manzon Allah SAW sai suka yi masa Sallama sai manzon Allah SAW ya ce: Mai ya taso ka ya Aba Hizyam? sai ya ce: wannan kuma sai ya daki cinyar hizyam da Hannunsa, sai ya ce: lallai ni ina jin tsoron kada tsufa ya cimmun ko kuma Mutuwa, shi yasa nake son nayi Wasiyya, kuma ni nace: cewa lallai farkon abunda zanyi Wasiyya da shi shi ne wannan Marayan nawada yake kan cinyata a bashi Raquma Xari, kuma muna kiranta a jahiliyya Kyautatawa, Sai Manzon Allah SAW yayi fushi har muka ga fushin a fuskarsa kuma yana Yana zaune sai ya durqusa kan Guiwoyinsa, kuma ya ce: A'a A'a Sadaqa Biyar ne, in kuma ba haka goma, in kuma ba haka ba to ashirin, in kuma ba haka ba Ashirin da Biyar in kuma ba haka ba Talatin in kuma ba haka ba Talatin da biyar idan kuma tayi yawa to arba'in" ya ce: sai suka yi masa bankwana da shi tare da Marayan akwai wani sanda, kuma da shi yake dukan Raqumin, sai Manzon Allah SAW ya ce: "Wanna sandar Mrayan tayi girma" Hanzala ya ce: sai ya kusanto dani zuwa Manzon Allah SAW sai ya ce: lallai ni ina da Yaya Maza ma'abota Gemu, da kuma qasa da haka kuma wannan shi ne Mafi qanqancinsu, ka roqa masa Allah, sai ya shafi kansa, kuma ya ce: "Allah yayi maka Al-barka" ko "An roqa maka Al-barka" Thayyal ya ce: kuma haqiqa naga Hanzala, ana zuwa da Mutum wanda fuskarsa ta kumbura ko dabba da Nononta ya kumbura sai yayi tofi a hannunsa kuma ya ce: da Sunan Allah sai ya sanya Hannunsa akan sa, kuma ya ce: akan wurin tafin Manzon Allah SAW sai ya shafeshi akai, kuma Thayyal ya ce: sai Kumburin ya tafi

Madogara

-مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. -المصباح المنير في غريب الشرح الكبير، لأحمد بن محمد بن علي الفيومي، الناشر: المكتبة العلمية – بيروت. -مختار الصحاح، لزين الدين أبو عبد الله محمد بن أبي بكر بن عبد القادر الحنفي الرازي، تحقيق: يوسف الشيخ محمد، نشر: المكتبة العصرية - الدار النموذجية، بيروت – صيدا، لطبعة: الخامسة، 1420هـ / 1999م. -سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، تأليف محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى، لمكتبة المعارف. -معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م. -الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني ومعه بلوغ الأماني من أسرار الفتح الرباني, أحمد بن عبد الرحمن بن محمد البنا الساعاتي, دار إحياء التراث العربي, الطبعة: الثانية.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com