Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce

عن سعد بن عبادة رضي الله عنه أنه قال: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّ أُمَّ سَعْدٍ مَاتَتْ، فَأَيُّ الصَّدَقَةِ أَفْضَلُ؟، قَالَ: «الْمَاءُ»، قَالَ: فَحَفَرَ بِئْرًا، وَقَالَ: هَذِهِ لِأُمِّ سَعْدٍ.
Daga Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: Ya Manzon Allah, lallai Ummu Sa'ad ta rasu, to wace sadaka ce tafi?. Ya ce: "Ruwa". Ya ce: Sai ya haƙa wata rijiya, ya ce: Wannan ga Ummu Sa'ad ce.
Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne ta jimillar hanyoyinsa
Sharhi

Mahaifiyar Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - ta rasu, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafificin nau'ikan sadaka dan ya yi sadaka dashi ga mahaifiyarsa? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ba shi labarin: Cewa mafificiyar sadaka ita ce ruwa, sai ya haƙa wata rijiya ya sanyata sadaka ga mahaifiyarsa.

Fa’idoji
  1. Bayanin cewa ruwa yana daga mafificin nau'ikan sadaka.
  2. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunawa da Sa'ad zuwa ga sadakar ruwa; domin shi ya fi gamewar anfani a cikin al'amuran addini da duniya, kuma saboda tsananin zafi da buƙata da ƙarancin ruwa.
  3. Nuni akan ladan sadaka yana zuwa ga mamata.
  4. Biyayyar Sa'ad ɗan Ubada - Allah Ya yarda da shi - ga mahaifiyarsa - Allah Ya yarda da su -.
Madogara

سنن أبي داود (3/ 109) (1681)، سنن النسائي (6/ 254) (3664)، سنن ابن ماجه (4/ 643) (3684)، شرح سنن أبي داود للعباد (204/ 19).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
WAƘAFI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com