Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FASHI

Hadisai 2

Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya

عن أَبِي أُمَامَةَ إِياسِ بنِ ثَعْلَبَةَ الحَارِثِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنِ اقْتَطَعَ حَقَّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ بِيَمِينِهِ، فَقَدْ أَوْجَبَ اللهُ لَهُ النَّارَ، وَحَرَّمَ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ» فَقَالَ لَهُ رَجُلٌ: وَإِنْ كَانَ شَيْئًا يَسِيرًا يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «وَإِنْ قَضِيبًا مِنْ أَرَاكٍ».
Daga Abu Umama Iyas ɗan Sa'alaba alHarisi - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga yin rantsuwa da Allah akan ƙarya kuma yana sane, hakan dan yankar haƙƙin wani mutum musulmi, domin cewa sakamkon hakan shi ne cancantar wuta, da haramta aljanna, kuma shi yana daga manyan zunubai. Sai wani mutum ya ce ya Manzon Allah: Koda abinda aka rantse akan shi ɗin wani abune dan kaɗan? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Koda hakan ya zama a itacen asuwakin da ake cira ne daga bishiyar ƙirya.

Fa’idoji
  1. Gargaɗarwa daga cin haƙƙoƙin wasu, da kwaɗayi akan maida su ga masu su duk ƙarancinsu kuwa, kuma hukuncin alƙali da kuskure ba ya halattawa mutum abinda bai kasance nasa ba ne.
  2. Nawawi ya ce: Kaurara haramcin haƙƙoƙin musulmai, kuma cewa shi babu banbanci tsakanin haƙƙi kaɗan da mai yawa; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Koda ya kasance kara ne na itaciyar ƙirya".
  3. Nawawi ya ce: Wannan uƙubar ga wanda ya yanki haƙƙin musulmi ne kuma ya mutu kafin tuba, amma wanda ya tuba ya yi nadama akan aikinsa kuma ya maida haƙƙin zuwa ga maishi ya warware daga gareshi kuma ya yi niyya akan cewa ba zai koma ba to haƙiƙa zunubin ya saraya daga gare shi.
  4. Alƙali ya ce: Keɓance musulmi dan kasancewarsu sune waɗanda ake yi wa magana kuma waɗanda ake mu'amala da su a shari'a a game, badan cewa wanin musulmi saɓaninsa ba ne, kai hukuncinsa (irin) hukuncinsane a cikin hakan.
  5. Nawawi ya ce: Karya shi ne bada labari daga abu akan saɓanin haƙiƙaninsa, da gangan ne ya kasance ko akan rafkanuwa, daidai ne bada labarin ya kasance daga abinda ya wuce ne ko abinda za'a fuskanta nan gaba.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 122) (137). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 239). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 309).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Duk waanda yayi zalunci dani daya na kasa, za'a ciccibo masa tun daga Kasan Bakwai"

عن عائشة رضي الله عنها عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ ظَلَم قِيدَ شِبْرٍ مِن الأرْضِ؛ طُوِّقَهُ مِن سَبْعِ أَرَضِين».
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da shi- daga Annabi ya ce: "Duk wanda ya sayar da dabino tayi 'Yaya to 'yayanta na mai sayarwa ne, sai in mai saya ya shardanta da shi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام, عبد الله بن عبد الرحمن البسام, تحقيق محمد صبحي حلاق, مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة الطبعة- العاشرة، 1426 هـ - 2006 م. - تطريز رياض الصالحين, فيصل بن عبد العزيز بن فيصل ابن حمد المبارك الحريملي النجدي, المحقق: د. عبد العزيز بن عبد الله آل حمد, الناشر: دار العاصمة للنشر والتوزيع، الرياض, الطبعة: الأولى، 1423 هـ - 2002 م. - شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام, إسماعيل الأنصاري, مطبعة السعادة, مصر, الطبعة الثالثة, 1392هـ, 1972م. - القاموس المحيط, مجد الدين أبو طاهر محمد بن يعقوب الفيروزآبادي, تحقيق: مكتب تحقيق التراث في مؤسسة الرسالة, بإشراف: محمد نعيم العرقسُوسي, الناشر: مؤسسة الرسالة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت - لبنان, الطبعة: الثامنة، 1426 هـ - 2005 م. - الصحاح تاج اللغة وصحاح العربية, أبو نصر إسماعيل بن حماد الجوهري الفارابي, تحقيق: أحمد عبد الغفور عطار, دار العلم للملايين – بيروت, الطبعة: الرابعة 1407 هـ‍ - 1987 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com