Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Mutum uku zan yi rigirma da su a ranar alƙiyama
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Nau'i uku na mutane zan yi rigima da su a ranar alƙiyama, duk wanda na zama abokin rigimarsa kuwa zan rinjaye shi: Na farko: Wanda ya rantse da Allah, ya yi alƙawari. sannan ya warware shi ya yi yaudara. Na biyu: Wanda ya saida ɗa akan cewa bawa ne, sai kuma ya ci kuɗinsa ya yi tasarrufi da ƙimarsa. Na uku: Wanda ya dauki ɗan ƙodago dan yin wani aiki, sai ya kammala masa aikin, amma bai biya shi kuɗin aikinsa ba.
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa, waɗanda Alkur’ani ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki (alwala) sabo da shi, da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
- Sindi ya ce: An ce: Ambatan ukun bawai dan keɓancewa ba ne; domin Shi Allah - Maɗaukakin sarki - Mai yin rigima ne da dukkanin azalimi, kai a'a dan tsanantawa ne akan waɗanan ukun.
- Ibnul Jauzi ya ce: Ɗa bawan Allah ne, duk wanda ya yi masa ta'addanci to mamallakinsa zai yi rigima da shi, wanda Shi ne Allah.
- Khaɗɗabi ya ce: Bautar da ɗa yana faruwa ne da al'amura biyu: Ya 'yanta shi sannan ya ɓoye hakan ko ya musanta. Na biyu: Yasa shi yi masa hidima akan dole bayan ya 'yanta shi, na farkonsu ya fi su tsanani. Na ce: Hadisin babin ya fi tsanani; domin cewa a cikinsa tare da ɓoye 'yantuwar ko musantawarsa aiki yana hukunta hakan na siyarwa da cin kuɗin, daga haka ne narkon ya zama ya fi tsanani.
صحيح البخاري (3/ 90) (2270). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام (4/ 252). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (4/ 108). مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (14/ 211).