Abu Katadah alAnsari - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana binciken wani wanda yake binsa bashi wanda yake ɓoye masa, sai ya same shi, sai wanda ake bi bashi ya ce: Lallai ni bani da kuɗi, kuma bani da dukiyar da zan biya bashinka. Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya sa ya rantse da Allah cewa shi bashi da dukiya? Sai ya rantse da Allah cewa shi mai gaskiya a abinda yake faɗa. Sai Abu Katadah - Allah Ya yarda da shi - ya ce lallai shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wanda yake so kuma yake farin ciki Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar alƙiyama da tsanace-tsanancanta da tsorace-tsoracenta, to ya yayewa wanda yake cikin ƙunci, shi ne cewa ya ƙara (lokaci) ya jinkirta neman bashin, ko ya sarayar da sashin bashin ko ma dukkansa.
- An so saurarawa wanda ke cikin ƙunci zuwa lokacin samun walwala, ko sarayar da bashin daga gare shi gaba ɗayansa ko sashinsa.
- wanda ya yayewa mumini baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa baƙin cikin ranar alƙiyama, sakamako yana daga jinsin aiki.
- Ka'ida (ita ce): Lallai cewa farillai sun fi nafilfili, sai dai a wasu lokuta nafila tana zama ta fi farilla, sarayar da bashi daga wanda ke cikin ƙunci nafila ne, kuma yi masa haƙuri da saurare da rashin neman to wannan farilla ne, nafila ta fi farilla a nan.
- Hadisin yana (bayani) a cikin haƙƙin wanda ke cikin ƙunci, to wannan an yi masa uzuri, amma mai taurin bashi wanda yana da dukiya, to haƙiƙa ya zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "Taurin bashin mawadaci zalinci ne".
صحيح مسلم (3/ 1196) (1563). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 457). الكاشف عن حقائق السنن(شرح المشكاة)، للطيبي (7/ 2172). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (16/ 392). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للقاري (5/ 1954). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 945).