Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

RIBA

Hadisai 5

Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu

عَنْ مَالِكِ بْنِ أَوْسِ بْنِ الْحَدَثَانِ أَنَّهُ قَالَ: أَقْبَلْتُ أَقُولُ مَنْ يَصْطَرِفُ الدَّرَاهِمَ؟ فَقَالَ طَلْحَةُ بْنُ عُبَيْدِ اللهِ وَهُوَ عِنْدَ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رضي الله عنهما: أَرِنَا ذَهَبَكَ، ثُمَّ ائْتِنَا، إِذَا جَاءَ خَادِمُنَا، نُعْطِكَ وَرِقَكَ، فَقَالَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: كَلَّا، وَاللهِ لَتُعْطِيَنَّهُ وَرِقَهُ، أَوْ لَتَرُدَّنَّ إِلَيْهِ ذَهَبَهُ، فَإِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «الْوَرِقُ بِالذَّهَبِ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ، وَالْبُرُّ بِالْبُرِّ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ، وَالشَّعِيرُ بِالشَّعِيرِ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ، وَالتَّمْرُ بِالتَّمْرِ رِبًا، إِلَّا هَاءَ وَهَاءَ».
Daga Malik ɗan Aus ɗan Hadasan cewa shi ya ce: Na taho ina cewa waye zai canji dirhamomi? sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi alhali shi yana wurin Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da su - ya ce: Ka nuna mana zinarenka, sannan kazo mana, idan ɗan aikinmu ya zo, zamu baka azirfarka, sai Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: A'a, wallahi kodai ka ba shi azirfarsa, ko ka dawo masa da zinarensa, domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Tabi'i Malik ɗan Aus yana bada labari cewa shi ya kasance a wurinsa akwai zinarai, kuma yana son ya canja su da azirfofi, sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce masa: Ka bamu zinarenka dan na gansu! sannan ya ce da shi bayan ya yanke zai saya: Ka je Ka dawo, idan ɗan aikinmu ya zo bayannan dan mu baka dirhamomin, Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana halarce a wurin, sai ya yi inkarin wannan nau'in na mu'amala, kuma ya yi wa Ɗalha rantsuwa akan cewa ya bada azirfar a take, ko ya dawo masa da zinarensa wanda ya karba daga gare shi, kuma ya bayyana masa sababin hakan cewa Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa saida zinari da azirfa ko akasin hakan ya wajaba ya zama hannu da hannu nan take, inba haka bafa to wannan cinikin zai zama riba abin haramtawa, kuma bataccen ciniki, ba'a saida zinari da azirfa ko azirfa da zinari sai hanuu da hannu kuma karba ya tabbata, haka ba'a saida alkama da alkama ko wake da wake ko sha'ir da sha'ir ko dabino da dabino sai daidai wa daidaida awo da awo,

Fa’idoji
  1. Nau’ukan da aka ambata a cikin wannan hadisin guda biyar ne: Zinare da azirfa da alkama da wake da sha'ir da dabino, idan ciniki ya tabbata a su sinfin to babu makawa dan inagancin cinikin daga sharuɗɗa biyu: Karɓa a majalasin ƙulla cinikin, da kuma daidaito a awo, kamar zinare da zinare, inba haka bafa zai zama riba ta fifiko, idan sun saɓa kamar azirfa da alkama misali to sharaɗi ɗaya ne dan ingancin ƙulla cinikin, shi ne karɓar kuɗin a majalasin ƙulla cinikin, inba haka bafa zai zama riba ta jinkiri.
  2. Ana nufi da majalasin ƙulla ciniki: Gurin ciniki, daidai ne sun kasance a zaune, ko suna tafiya, ko akan abin hawa, kuma ana nufi da rabuwa abinda ake ɗauka a matsayin rabuwa a al'ada tsakaknin mutane.
  3. Hani a cikin hadisin ya ƙunshi dukkan nau'ikan zinaren da aka kera da wasunsu, da kuma dukkan azirfar da aka kera da wacce ba'a kera ba.
  4. Takardun kudade a wannan zamanin yana tabbata a cikinsu abinda yake tabbata acikin saida zinare da a zirfa, wato idan ka yi nufin canja wani kuɗi da wani kuɗin daban kamar riyal da dirhami to fifiko ya halatta da abinda masu ƙulla cinikin suka yarda da shi, sai dai karɓa yana wajaba a wurin siyarwar, inba haka ba to cinikin ya ɓaci, mu'amalar ta zama riba wacce haramta.
  5. Mu'amaloli na riba basa halatta, kuma ƙullasu ɓatacce ne koda masu cinikin sun yarda; domin Musulunci yana kiyaye haƙƙin mutum da haƙƙin zamantakewa koda shi ya haƙura na shi.
  6. Hani daga abin ƙi da kuma hana shi ga wanda zai iya hakan.
  7. Anbatan dalili a lokacin inkarin abin ƙi, kamar yadda Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya yi.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 68) (2134). صحيح مسلم (3/ 1209) (1586). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 28). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص496).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- "Annabi ya hana saida Zinare da Azurfa Bashi

عن أبي المنهال قال: «سألت البراء بن عازب، وزيد بن أرقم، عن الصَّرْفِ؟ فكل واحد يقول: هذا خير مني. وكلاهما يقول: نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن بيع الذهب بالوَرِقِ دَيْنَاً».
An Rawaito daga Abu Minhal ya ce: "Na tambayi Al-barra'a Bn Azib, da kuma Zaid Bn Arkam, game da Canji, sai kowane daya daga cikinsu yana cewa: Wannan Al-khairi ne gareni, kuma dukkansu suna cewa: Annabi ya hana saida Zinare da Azurfa Bashi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف عبد الله الفوزان، طبعة دار ابن الجوزي -الطبعة الأولى- 1428 - توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، تأليف عبد الله البسام، مكتبة الأسدي -مكة المكرمة- الطبعة الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام، للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية، 1392هـ. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام، تحقيق محمد صبحي حسن حلاق -مكتبة الصحابة- الشارقة - الطبعة العاشرة- 1426.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Manzon Allah ya hana Sayar da Azurfa da Azurfa, da Zinare da Zinare, Sai dai dai da dai dai, Kuma ya Umarce mu Mu sayar da Azurfa da Zinare, duk yadda muka so, kuma mu sayi Zinare da Azurfa yadda Muka so"

عن أبي بكرة رضي الله عنه قال: «نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن الفضة بالفضة، والذهب بالذهب، إلا سَوَاءً بسوَاءٍ، وأمرنا أن نشتري الفضة بالذهب، كيف شئنا. ونشتري الذهب بالفضة كيف شئنا، قال: فسأله رجل فقال: يدا بيد؟ فقال: هكذا سمعت».
An rawaito daga Abu Bakara -ALlah ya yarda da shi- ya ce: "Manzon Allah ya hana Sayar da Azurfa da Azurfa, da Zinare da Zinare, Sai dai dai da dai dai, Kuma ya Umarce mu Mu sayar da Azurfa da Zinare, duk yadda muka so, kuma mu sayi Zinare da Azurfa yadda Muka so, ya ce: sai wani mutum ya tambaye shi sai ya ce: Hannu da Hannu? sai ya ce: haka naji"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام، للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية 1392هـ. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام، تحقيق محمد صبحي حسن حلاق -مكتبة الصحابة- الشارقة، الطبعة العاشرة، 1426ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wayyo, Wayyo, Wannan tsantantsar ribace, kada kayi, kuam sai dai idan kanason ka saya to ka siyar da dabinonka da wani cinikin daban, sannan ka saya da kudin

عن أبي سعيد الخدري- رضي الله عنه-: جاء بلال إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم بتمر بَرْنِيٍّ، فقال له النبي صلى الله عليه وسلم : «من أين لك هذا؟» قال بلال: كان عندنا تمر رديء، فبعتُ منه صاعين بصاع ليطعم النبي صلى الله عليه وسلم . فقال النبي صلى الله عليه وسلم عند ذلك: «أَوَّهْ، أَوَّهْ، عَيْنُ الربا، عين الربا، لا تفعل، ولكن إذا أردت أن تشتري فَبِعِ التمرَ ببيع آخر، ثم اشتر به».
Daga Abu Sa'id Alkhudri -Allah yarda da shi- :Bilal ya zo wajen Annabi da Dabino Birni, sai Annabi ya ce da shi "ina ka samo wannan? Sai Bilal ya ce: ya kasance Muna da Dabino ne Mara kyau sai na saida shi da kwano biyu da kuma daya don in ciyar da Annabi sai Annabi yace lokacin:m "Wayyo, Wayyo, Wannan tsantantsar ribace, kada kayi, kuam sai dai idan kanason ka saya to ka siyar da dabinonka da wani cinikin daban, sannan ka saya da kudin"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Bilal ya zo wajen Annabi da Dabino Biryani mai kyau, sai Annabi yayi mamakin kyawun kansa kuma ya ce: Daga ina wannan? sai Bilal ya ce: ina da wani Dabino ne, sai na bada kwano biyu na mara kyau aka bani kwano daya na wannan mai kyau, don ya kasance na kawowa Annanbi daga cikinsa, sai hakan ya girmama ga Annabi kuma yayi kash da hakan, domin hakan Sabo ne a wajensa kuma shi ne Mafi girman Musibu, kuma ya ce: wannan aikin naka, shi ne tsantsan Riba wacce aka haramta, to kada kayi hakan, sai dai idan kanaso sai ka canza mara kyawun da kudi ta hanyar siyarwa, sannan kudin sai ka siyi Dabinon da shi mai kyau, to wannan hanya ita halas ce kana iya yinta, don nisantar fadawa cikin haramun. "Taisir Allam Sharhin Umdatu Al'ahkam" (Shafi/568)

Madogara

- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه. - خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام - فيصل بن عبد العزيز بن فيصل ابن حمد المبارك الحريملي النجدي - الطبعة: الثانية، 1412 هـ - 1992 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne

عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الذَّهَبُ بِالذَّهَبِ، وَالْفِضَّةُ بِالْفِضَّةِ، وَالْبُرُّ بِالْبُرِّ، وَالشَّعِيرُ بِالشَّعِيرِ، وَالتَّمْرُ بِالتَّمْرِ، وَالْمِلْحُ بِالْمِلْحِ، مِثْلًا بِمِثْلٍ، سَوَاءً بِسَوَاءٍ، يَدًا بِيَدٍ، فَإِذَا اخْتَلَفَتْ هَذِهِ الْأَصْنَافُ، فَبِيعُوا كَيْفَ شِئْتُمْ، إِذَا كَانَ يَدًا بِيَدٍ».
Daga Ubadah ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana hanyar yin inagntaccen ciniki a cikin nau’ukan da riba take shiga cikinsu (abubuwa) guda shida sune: Zinare, da azirfa, da alkama, da sha'ir, da dabino, da gishiri, idan sun kasance daga irin nau'in ne kamar saida zinare da zinare azirfa da azirfa... to babu makawa daga sharuɗɗa biyu: Na farko: Tabbatar daidaituwa a cikin awon sikeli ne, idan ya kasance abin aunawa ne na sikeli kamar zinare da azirfa, ko samun daidaito a awo idan ya kasance abin aunawa ne na kwano kamar alkama da sha'ir da dabino da kuma gishiri. Na biyu: Mai siyen ya karɓi abin siyarwar shi kuma mai siyarwar ya karɓi kuɗin, hakan (ya zama) a gurin da akayi cinikin. Idan waɗannan nau’ukan suka saɓa kamar saida zinare a bada azirfa, da dabino a bada alkama misali, to cinikin ya halatta da sharaɗi ɗaya, shi ne mai siyarwar ya karɓi kuɗin shi kuma mai siyen ya karɓi abin siyan a gurin da aka yi cinikin, inba haka bafa to cinikin ɓatacce ne, kuma sun faɗa cikin ribar da aka haramta, mai siyen da mai siyarwar duk ɗaya ne a hakan.

Fa’idoji
  1. Bayanin dukiyoyin da riba take shiga cikinsu da kuma yadda ciniki yake kasancewa a cikinsu.
  2. Hani daga cinikin riba.
  3. Takardun kuɗi suna da hukuncin zinare da azirfa a cikin illar riba.
  4. Siye da siyarwar nau’ukan da riba take shiga cikinsu guda shida suna da halaye: 1- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa daga jinsinsa, kamar zinare da zinare dabino da dabino... to dan (cinikin) ya zama ingantacce an sharɗanta sharuɗɗa biyu: Samun daidaituwa a cikin awon sikeli ko awon kwano, da kuma karɓa a gurin da aka yi cinikin. 2- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa wanda ba jinsinsa ba tare da cewa illar ta zama iri ɗaya, kamar zinare da azirfa, da alkama da sha'ir to a hakan an sharɗanta karɓa, banda samun daidaituwa. 3- A saida abinda riba take shiga cikinsa da abinda riba take shiga cikinsa wanda bana jinsinsa ba tare da samun banbancin illar, to a hakan ba'a sharɗanta karɓa ko daidaituwa ba kamar saida zinare da dabino.
  5. Siyrawa da siyan nau’uka waɗanda riba bata shiga cikinsu, ko ɗayansu riba na shiga cikinsa ɗayan kuma riba bata shiga cikinsa; to ba'a sharɗanta komai ba, ba hannu da hannu ba ba kuma daidaito a awo ba, kamar saida fili da zinare.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1210) (1587). فيض القدير (3/ 571). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (27/ 623).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com