Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SHARUƊAN CINIKI

Hadisai 1

Lallai cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a garesu- "cewa lallai Annabi ya hana cin kudin kare, Da Sadakin karuwanci, da kuma ladan boka".

عن أبي مسعود رضي الله عنه «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم نهى عن ثمن الكلب، ومَهْرِ البغي، وحُلْوَانِ الكَاهِنِ».
Daga Dan Mas'ud-Allah ya yarda da shi- : "cewa lallai Annabi ya hana cin kudin kare, Da Sadakin karuwanci, da kuma ladan boka".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Hanyoyin neman Arziki na Halak suna da yawa, kuma Allah ya sanya su a maimakon wasu Munanan hanyoyiwadanda basu da Albarka, to yayin da hanyoyin farko ta wadatar da Mutum ga barin hanyoyin na biyun, kuma da kasancewa hanyoyin na biyun barnarsu ta girmama kuma babu wani amfani da yake biye da shi, sai Shariah ta Haramta miyagun hanyoyin baki daya, wadan nan sunehanyoyi Ukun: 1.Sai da Kare: don shi Najasa ne kuma kazanta ne. 2.kuma da abinda karuwa ta karba na ladan fajircinta, wanda da shi take bata Duniyarta da Lahirarta. 3.Kwatankwacinsa abinda Boka da 'Yan Bori da Masu batar da Mutane, daga cikin wadanda suke Da'awar Gaibu da kuma iko kan dukkan Halittu, suke damfarar Mutane -Da Karyarsu- don su wawashe musu Dukiyoyinsu, sai su ci dukiyar ta hanyar barna, kuma dukkan wadan nan hanyoyi sun munana kuma sun haramta, kuma bai halatta a aikata su, haka kuma bada wani lada akansu, kuma Allah ya canza musu da Mafi Alkairi halattacce kuma mai tsafta.

Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب - الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، للشيخ ابن عثيمين- المكتبة الإسلامية، القاهرة، تحقيق صبحي رمضان وأم إسراء بيومي، الطبعة الأولى، 1427ه. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام، للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية، 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام، تحقيق محمد صبحي حسن حلاق -مكتبة الصحابة- الشارقة، الطبعة العاشرة، 1426ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com