عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما قَالَ: إِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ أَنْزَلَ: {وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللهُ فَأُولَئِكَ هُمِ الْكَافِرُونَ} [المائدة: 44] وَ {فَأُولَئِكَ هُمُ الظَّالِمُونَ} [المائدة: 45] وَ {فَأُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ} [المائدة: 47] ، قَالَ: قَالَ ابْنُ عَبَّاسٍ: أَنْزَلَهَا اللهُ فِي الطَّائِفَتَيْنِ مِنَ اليَهُودِ، وَكَانَتْ إِحْدَاهُمَا قَدْ قَهَرَتِ الأُخْرَى فِي الجَاهِلِيَّةِ، حَتَّى ارْتَضَوْا وَاصْطَلَحُوا عَلَى أَنَّ كُلَّ قَتِيلٍ قَتَلَتْهُ العَزِيزَةُ مِنَ الذَّلِيلَةِ فَدِيَتُهُ خَمْسُونَ وَسْقًا، وَكُلَّ قَتِيلٍ قَتَلَتْهُ الذَّلِيلَةُ مِنَ العَزِيزَةِ فَدِيَتُهُ مِائَةُ وَسْقٍ، فَكَانُوا عَلَى ذَلِكَ حَتَّى قَدِمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ المَدِينَةَ، وَذَلَّتِ الطَّائِفَتَانِ كِلْتَاهُمَا لِمَقْدَمِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ورَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمَئِذٍ لَمْ يَظْهَرْ، وَلَمْ يُوطِئْهُمَا عَلَيْهِ، وَهُوَ فِي الصُّلْحِ، فَقَتَلَتِ الذَّلِيلَةُ مِنَ العَزِيزَةِ قَتِيلًا، فَأَرْسَلَتِ العَزِيزَةُ إِلَى الذَّلِيلَةِ: أَنِ ابْعَثُوا إِلَيْنَا بِمِائَةِ وَسْقٍ، فَقَالَتِ الذَّلِيلَةُ: وَهَلْ كَانَ هَذَا فِي حَيَّيْنِ قَطُّ دِينُهُمَا وَاحِدٌ، وَنَسَبُهُمَا وَاحِدٌ، وَبَلَدُهُمَا وَاحِدٌ، دِيَةُ بَعْضِهِمْ نِصْفُ دِيَةِ بَعْضٍ؟ إِنَّا إِنَّمَا أَعْطَيْنَاكُمْ هَذَا ضَيْمًا مِنْكُمْ لَنَا، وَفَرَقًا مِنْكُمْ، فَأَمَّا إِذْ قَدِمَ مُحَمَّدٌ فَلَا نُعْطِيكُمْ ذَلِكَ، فَكَادَتِ الحَرْبُ تَهِيجُ بَيْنَهُمَا، ثُمَّ ارْتَضَوْا عَلَى أَنْ يَجْعَلُوا رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَيْنَهُمْ، ثُمَّ ذَكَرَتِ العَزِيزَةُ، فَقَالَتْ: وَاللهِ مَا مُحَمَّدٌ بِمُعْطِيكُمْ مِنْهُمْ ضِعْفَ مَا يُعْطِيهِمْ مِنْكُمْ، وَلَقَدْ صَدَقُوا، مَا أَعْطَوْنَا هَذَا إِلَّا ضَيْمًا مِنَّا، وَقَهْرًا لَهُمْ، فَدُسُّوا إِلَى مُحَمَّدٍ مَنْ يَخْبُرُ لَكُمْ رَأْيَهُ: إِنْ أَعْطَاكُمْ مَا تُرِيدُونَ حَكَّمْتُمُوهُ، وَإِنْ لَمْ يُعْطِكُمْ حَذِرْتُمْ فَلَمْ تُحَكِّمُوهُ، فَدَسُّوا إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَاسًا مِنَ المُنَافِقِينَ لِيَخْبُرُوا لَهُمْ رَأْيَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمَّا جَاءَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخْبَرَ اللهُ رَسُولَهُ بِأَمْرِهِمْ كُلِّهِ وَمَا أَرَادُوا، فَأَنْزَلَ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ {يَا أَيُّهَا الرَّسُولُ لَا يَحْزُنْكَ الَّذِينَ يُسَارِعُونَ فِي الْكُفْرِ مِنَ الذِينَ قَالُوا آمَنَّا} [المائدة: 41] إِلَى قَوْلِهِ: {وَمَنْ لَمْ يَحْكُمْ بِمَا أَنْزَلَ اللهُ فَأُولَئِكَ هُمِ الْفَاسِقُونَ} [المائدة: 47] ثُمَّ قَالَ فِيهِمَا: وَاللهِ نَزَلَتْ، وَإِيَّاهُمَا عَنَى الله عَزَّ وَجَلَّ.
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da:
{Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai} [al-Ma'idah: 44], da {Waɗannan sune azzalimai} [al-Ma'ida: 45] da kuma {Waɗannan sune fasiƙai} [al-Ma'ida: 47].
ya ce: Ibnu Abbas ya ce: Allah Ya saukar da ita ne saboda ƙungiyoyi biyu daga cikin Yahudawa, ɗayarsu ta kasance ta rinjayi ɗayar a lokacin Jahiliyya, har suka yadda suka yi sulhu akan cewa dukkanin wadda aka kashe to wacce ta yi rinjayen (babbar kabilar) ta kashe shi daga cikin ƙasƙantacciya (wacce aka yi nasara a kanta) to diyyarsa ita ce Wusƙi hamsin, kuma dukkanin wadda aka kashe wadda ƙasƙantacciyar ta kashe shi daga mai rinjayen to diyyarsa ita ce Wusƙi ɗari, sun kasance akan haka har Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, dukkanin ƙungiyoyi biyun suka miƙa wuya ga zuwan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wannan lokacin bai yi rinjaye galaba, kuma bai haɗasu a kansa ba, shi yana cikin sulhu, sai ƙasƙantacciyar ta kashe wani daga cikin mai rinjayan, sai mai rinjayen ta aika zuwa gurin ƙasƙantacciyar: Ku aiko mana da Wusƙi ɗari, sai ƙasƙantacciyar ta ce: Shin wannan ya kasance ne a cikin ƙabilu biyu kawai Addininsu ɗaya, nasabarsu ɗaya, garinsu ɗaya, diyyar sashinsu rabin diyyar sashi ce? Mu ɗin nan mun baku wannan ne kawai dan zalincinku a garemu, da rinjayen da kuka yi mana, amma tunda (Annabi) Muhammad ya zo to baza mu baku hakan ba, sai yaƙi ya kusa ya kunnu a tsakaninsu, sannan suka yarda su sanya Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsakaninsu, sannan wacce ta yi galabar ta ambata sai ta ce: Wallahi (Annabi) Muhammad ba zai baku daga cikinku ninkin abin da suke basu daga garesu ba, kuma haƙiƙa sun yi gaskiya, ba su bamu wannan ba sai dan zalincin da muke yi, da kuma rinjayarsu da muka yi, dan haka ku yi dassi zuwa ga (Annabi) Muhammad wanda zai binciko muku ra'ayinsa: Idan ya baku abin da kuke so to sai ku sanya shi mai hukunci, idan kuma bai baku ba sai ku kiyaye shi, ba zaku sanya shi mai hukunci ba, sai suka yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dassin wasu mutane daga cikin munafukai dan su basu labarin ra'ayin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai Allah Yaba ManzonSa labarin gabaɗayan al'amarinsu da kuma abin da suka yi nufi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Yakai Manzo kada waɗanda suka yi gaggawa cikin kafirci daga waɗanda suka ce mun yi imani su baƙanta maka rai}[al-Ma'ida: 41] har zuwa faɗinSa: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47] sannan ya ce: Wallahi ta sauka ne a cikin sha'aninsu, kuma sune Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yake nufi.
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
A cikin Yahudawan Madina akwai Banu Ƙuraiza da Banun Nadhir, ɗaya ta kasance ta rinjayi ɗayar a lokacin Jahiliyya, sai suka yarda da sulhu akan cewa duk wanda babbar Kabila (wato wacce ta yi nasara) ta kashe cikin kowacce da aka rinjaya to diyyarsa ita ce Wusƙi hamsin kawai, kuma dukkanin wanda aka kashe daga cikin maɗaukakiyar Kabila wanda mai raunin ta kashe shi to diyyarsa ita ce Wusƙi ɗari, shi kuma Wusƙi shi ne Sa'i sittin. sai suka kasance akan haka har Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina yana mai hijira, kuma ƙungiyoyi biyun suka miƙa wuya ga zuwansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali shi - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - a wannan lokacin bai yi nasara akan maƙiyansa ba, bai rijayesu akan yi masa biyayya ba; domin hakan ya kasance a farkon hijira ne, shi kuwa yana cikin sulhu. Sai ƙasƙantacciyar kabilar (wacce aka yi nasara akanta) ta kashe wani mutum daga cikin maɗaukakiyar (wacce ta yi nasara), sai maɗaukakiyar ta aikawa ƙasƙantacciyar: Cewa ku aiko mana da Wusƙi ɗari kamar yadda muka yi ittifaƙi, sai ƙasƙantacciyar ta ce: Shi wannan ya kasance ne a cikin ƙabilu biyu kawai, Addininsu ɗaya, nasabarsu ɗaya, garinsu ɗaya, diyyar sashinsu rabin diyyar sashi?! lallai mu muna baku wannan ne dan zalintarmu da kuke yi, da kuma tsoronku, amma yayin da (Annabi) Muhammad ya ya zo to ba zamu baku haka ba har abada. Sai yaƙi ya kusa barkewa a tsakaninsu, sannan suka yarda su sanya Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hukunci tsakaninsu, sannan ita babbar kabilar ta lura, sai ta ce: Wallahi Muhammad ba zai baku daga garesu ninkin abin da suke basu daga gareku ba, kuma haƙiƙa sun yi gaskiya, basu bamu wannan ba sai dan mun zalince su, da kuma rijayarsu, to ku aika zuwa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanda zai zo musu da ra'ayinsa a ɓoye, idan ya baku abin da kuke so sai ku sanya shi mai hukunci, idan kuma bai baku abin da kuke sha'awa ba sai ku barshi bazaku sanya shi mai hukunci tsakaninku ba. Sai suka aika wasu mutane daga cikin munafukai zuwa gurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan su san ra'ayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Allah Ya saukar da wahayi kuma Ya bawa ManzonSa labari da al'amarinsu gabaɗayansa da abin da suka yi nufi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da Suratul Ma'idah daga faɗinSa: {Yakai wannan Manzo, kar waɗannan da suke gaggawa cikin kafirci su baƙanta maka rai, daga cikin waɗanda sukace: "Mun yi imani"}[al-Ma'idah: 41]. Har zuwa faɗinSa: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47]. Sannan Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Wallahi faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - a sha'aninsu ne ya sauka: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai}[al-Ma'idah: 44]. Da {...Waɗanan sune azzalimai}[al-Ma'idah: 45] Da kuma {...Waɗanann sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47], kuma sune Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yake nufi.
Fa’idoji
- Yahudawa sun san gaskiyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma amanarsa.
- Makircin Yahudawa da kuma zalincinsu har akan kansu.
- Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya bada labarin cewa Yahudawa wulaƙanci ya tabbata garesu a duniya da kuma azaba mai raɗaɗi a lahira.
- Rashin yin hukunci da abin da Allah Ya saukar da kuma kin yarda da hukuncin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dalili ne akan kafirci da zalinci da kuma fasiƙanci.
- Haɗarin munafukai da kuma taimakekeniyarsu tare da Yahudawa.
Madogara
مسند أحمد (4/ 88) (2212).
النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 972،978،702،1017،305).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ مِنْبَرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ رَجُلٌ: مَا أُبَالِي أَلَّا أَعْمَلَ عَمَلًا بَعْدَ الإِسْلَامِ إِلَّا أَنْ أُسْقِيَ الحَاجَّ، وَقَالَ آخَرُ: مَا أُبَالِي أَلَّا أَعْمَلَ عَمَلًا بَعْدَ الإِسْلَامِ إِلَّا أَنْ أَعْمُرَ المَسْجِدَ الحَرَامَ، وَقَالَ آخَرُ: الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ أَفْضَلُ مِمَّا قُلْتُمْ، فَزَجَرَهُمْ عُمَرُ، وَقَالَ: لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ عِنْدَ مِنْبَرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ يَوْمُ الجُمُعَةِ، وَلَكِنْ إِذَا صَلَّيْتُ الجُمُعَةَ دَخَلْتُ فَاسْتَفْتَيْتُهُ فِيمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ، فَأَنْزَلَ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: {أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ} [التوبة: 19] الآيَةَ إِلَى آخِرِهَا.
Daga Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce:
Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ambaci cewa shi yana zaune a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wani mutum yana cewa: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in shayar da mai aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa. Sai Umar Ibnul Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi- ya yi musu tsawa saboda ɗaga muryarsu da suka yi a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma safiyar ranar Juma'a ce, sai dai idan na yi sallar Juma'a zan shiga in tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da:
{Shin, kun mayar da shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Tauba: 19].
Fa’idoji
- Fifikon ayyuka a lada da sakamako.
- Fifikon ayyuka gwargwadan abin da shari'a ta zo da shi, bawai gwargwadan ƙoƙarin mutane ba.
- Falalar Jihadi a tafarkin Allah da sharaɗin yin imani da Allah ne da kuma ranar lahira.
- Nawawi ya ce: A cikinsa akwai karahiyar ɗaga murya a cikin masallatai a ranar Juma'a da waninta, kuma mutum kada ya ɗaga murya da ilimi ne ko da waninsa a lokacin taruwar mutane dan yin sallah saboda abin da ke cikinsa na takura musu da kuma masu yin sallar da kuma masu yin zikiri.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1499) (1879).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (3/ 720).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (32/ 395).
النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 897).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ رَفَعَهُ: فِي قَوْلِ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ: {وَمَنْ يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍ بِظُلْمٍ نُذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ} [الحج: 25] قَالَ: «لَوْ أَنَّ رَجُلًا هَمَّ فِيهِ بِإِلْحَادٍ وَهُوَ بِعَدَنِ أَبْيَنَ لَأَذَاقَهُ اللَّهُ عَذَابًا أَلِيمًا».
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ruwaito shi Marfu'i: A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Abdullahi ɗan mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambata a cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Duk wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci to zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi}.
[al-Hajj: 25], ya ce: Da ace wani daga cikin mutane zuciyarsa zata zantar masa cewa ya yi nufin aikata wani mummunan aiki a cikin Haramin Makka wanda zai halatta abinda Allah Ya haramta masa a cikinsa na haram da harshe ne ko kisa da gangan to cewa hakan zalinci ne, kuma da a ce ƙudirin niyyar a birnin Adan ne a cikin (kasar) Yaman to lallai shi mai cancantar Allah Ya azabtar da shi ne da azaba mai raɗaɗi saboda hakan, koda kuwa bai aikata shi ba, niyyar hakan kawai ta ishe shi .
Fa’idoji
- Bayanin matsayin da harami ya kebanta da shi da kuma girmama shi .
- Al-Sa'adi ya ce: A cikin wannan ayar mai girma, akwai wajabcin ganin alfarmar Harami, da tsananin girmama shi, da gargaɗarwa daga nufin yin saɓo a cikinsa da kuma aikata (saɓon).
- Al-Dahhak ya ce: Lallai mutum zai yi niyyar aikata kuskure a Makka alhali shi yana wata ƙasar daban sai arubuta masa (laifin) alhali bai aikata laifin ba.
Madogara
مسند أحمد (7/ 155) (4071).
المستدرك على الصحيحين للحاكم (2/ 420) (3461).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (10/ 52).
جامع العلوم والحكم (2/ 327).
النهاية في غريب الحديث والأثر ( ص 829،1012، 597).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنْتُ سَاقِيَ القَوْمِ فِي مَنْزِلِ أَبِي طَلْحَةَ، وَكَانَ خَمْرُهُمْ يَوْمَئِذٍ الفَضِيخَ، فَأَمَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُنَادِيًا يُنَادِي: أَلاَ إِنَّ الخَمْرَ قَدْ حُرِّمَتْ، قَالَ: فَقَالَ لِي أَبُو طَلْحَةَ: اخْرُجْ، فَأَهْرِقْهَا، فَخَرَجْتُ فَهَرَقْتُهَا، فَجَرَتْ فِي سِكَكِ المَدِينَةِ، فَقَالَ بَعْضُ القَوْمِ: قَدْ قُتِلَ قَوْمٌ وَهِيَ فِي بُطُونِهِمْ، فَأَنْزَلَ اللَّهُ: {لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُوا} [المائدة: 93] الآيَةَ.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana cikin shayar da wanda yake cikin gidan mijin babarsa Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi -, giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, shi ne cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yansa kafin ya zama ɗanye, sai ga mai kira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita, ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai giyar ta kwarara a lungunan Madina, sai wasu daga mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe (a jihadi) wasu sahabbai kafin haramtata alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da:
{Babu laifi akan waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka dandana} [al-Ma'ida: 93] Aya. Wato: Babu zunubi akan waɗanda suka yi imani a cikin abinda suka dandana kuma suka sha na giya kafin haramtata.
Fa’idoji
- Falalar Abu Ɗalha da sahabbai - Allah Ya yarda da su -, dan sun amsa umarnin Allah da gaggawa kuma ba tare da tambaya ba, wannan shi ne abinda ya kamata ga musulmi na gaskiya.
- Giya: Ita Suna ne da ya ƙunshi dukkan abin da yake sa maye.
- Fadikh: wani abin sha ne da ake yinsa daga 'ya'yan dabino da kuma bushasshensa ba tare da wuta ta taɓa shi ba, Busr kuwa: Shi ne 'ya'yan dabino kafin ya zama ɗanye.
- Ibnu Hajar ya ce: Muhallab ya ce: Kawai an zubar da giyar ne a hanya dan bayyanar da ƙiyayyarta da kuma bayyanar da barinta, hakan ya fi rinjaye a maslaha daga cutuwa da zubar da ita a hanya.
- Bayanin rahamar Allah ga bayinSa, kuma cewa Shi ba Ya yin hisabi akan aiki kafin saukar da hukunci.
- Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta giya; dan abinda ke cikinta na nau’ukan barna da zasu sa cuta ga hankali da kuma dukiya, saboda da ita ne mutum yake aikata zunubai da yawa; dan gushewar hankalinsa.
Madogara
صحيح البخاري (3/ 132) (2464).
صحيح مسلم (3/ 1570) (1980).
النهاية في غريب الحديث والأثر (709) (1006).
فتح الباري لابن حجر (1/ 133).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (4/ 267).
Wannan hadisi a HadeethEnc.com