Lallai waxanda suka kai Matsayin cika a cikin Falalar Addini da Halayya daga cikin Maza akwai da yawa daga cikinsu akwai wanda yakai Matakin cika ta Al-ada Kamar Malamai da Mutanen kirki da Waliyyai, akwai daga cikin su akwai wanda ya wuce matakin cika kamar Annabwa, amma Matan da suka cika su ne kaxan kwarai kuma waxanda suke gaba Asiya Matar Fir'auna ita Asiya Bint Muzahim wacce Allah ya buga Misali da ita a cikin cikar Imani, sai ya ce: "Kuma Allah ya buga Misali ga waxanda sukai Imani Matar fir'auna" Saboda tayi Imani da Annabi Musa lokacin da yai Nasara kan Masu Sihirin fir'auna, kuma yayin da fir'auna ya san ta yi Imani sai yayi mata Azaba Mai tsanani har zuwa lokacin da ta Mutu tana riqe da Imaninta, amma ta biyu ita ce Maryam Bint Imran wacce Allah ya buga Misali wajen kare kanta, da kuma cikar Ibadarta, sannan SAW ya ce: "Kuma falalar Aisha kan sauran Mata kamar fifikon Tharid kan sauran Abinci" Tharid shi ne mafi daxin abincin Larabawa kuma anayinsa ne da gurasa da kuma nama, to Aisha a Fifikon ta kan Mata kamar Fifikon wancan Tharid xin wanda shi ne mafi daxin abinci kan Sauran Abinci
صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد بن موسى الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة محمد قاسم، راجعه: الشيخ عبد القادر الأرناؤوط، عني بتصحيحه ونشره: بشير محمد عيون، الناشر: مكتبة دار البيان، دمشق - الجمهورية العربية السورية، مكتبة المؤيد، الطائف - المملكة العربية السعودية، عام النشر: 1410 هـ - 1990 م. إكمال المعلم بفوائد مسلم لعياض بن موسى بن عياض بن عمرون اليحصبي السبتي، المحقق: الدكتور يحيى إسماعيل، الناشر: دار الوفاء للطباعة والنشر والتوزيع، مصر، الطبعة: الأولى، 1419 هـ - 1998 م.