Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ تَسُبُّوا أَصْحَابِي، فَلَوْ أَنَّ أَحَدَكُمْ أَنْفَقَ مِثْلَ أُحُدٍ ذَهَبًا مَا بَلَغَ مُدَّ أَحَدِهِمْ، وَلاَ نَصِيفَهُ».
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga zagin sahabbai, musamman ma marigaya na farko daga muhajirai da mutanen Madina; kuma ya bada labarin cewa shi da wani daga mutane zai ciyar da kwatankwacin dutsen Uhudu na zinari ladansa ba zai kai ladan ciyarwar wani daga sahabbai ba mudu na abinci ko rabinsa ba - mudu shi ne cikin tafuka biyu na mutum matsakaicin halitta -; hakan dan ƙarin ikhlasinsu, da gaskiyar niyyarsu, da rigayar ciyarwarsu da yaƙinsu kafin buɗe Makka inda tsananin buƙatuwa gare shi take.

Fa’idoji
  1. Zagin sahabbai - Allah Ya yarda da su - haramun ne, kuma yana daga manyan zunubai.
Madogara

صحيح البخاري (5/ 8) (3673). صحيح مسلم (4/ 1967) (2540). عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لبدر الدين العيني (16/ 187). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي (16/ 93). الإفصاح عن معاني الصحاح، ليحيى بن هبيرة (8/ 70). نزهة النظر في توضيح نخبة الفكر في مصطلح أهل الأثر، لأحمد بن حجر العسقلاني (ص111).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
AƘIDA GAME DA SAHABBAI ALLAH YA ƘARA YARDA DA SU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com