Daga Abu Humaid al-Sa'idi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne».
Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.
Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.