Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sahih al-Bukhari

Lamba 1014

Lamba 1014Littafi na 15, lamba 9
حَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ، قَالَ حَدَّثَنَا إِسْمَاعِيلُ بْنُ جَعْفَرٍ، عَنْ شَرِيكٍ، عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ، أَنَّ رَجُلاً، دَخَلَ الْمَسْجِدَ يَوْمَ جُمُعَةٍ مِنْ بَابٍ كَانَ نَحْوَ دَارِ الْقَضَاءِ، وَرَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَائِمٌ يَخْطُبُ، فَاسْتَقْبَلَ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَائِمًا ثُمَّ قَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ هَلَكَتِ الأَمْوَالُ وَانْقَطَعَتِ السُّبُلُ، فَادْعُ اللَّهَ يُغِيثُنَا فَرَفَعَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يَدَيْهِ ثُمَّ قَالَ ‏"‏ اللَّهُمَّ أَغِثْنَا، اللَّهُمَّ أَغِثْنَا، اللَّهُمَّ أَغِثْنَا ‏"‏‏.‏ قَالَ أَنَسٌ وَلاَ وَاللَّهِ مَا نَرَى فِي السَّمَاءِ مِنْ سَحَابٍ، وَلاَ قَزَعَةً، وَمَا بَيْنَنَا وَبَيْنَ سَلْعٍ مِنْ بَيْتٍ وَلاَ دَارٍ‏.‏ قَالَ فَطَلَعَتْ مِنْ وَرَائِهِ سَحَابَةٌ مِثْلُ التُّرْسِ، فَلَمَّا تَوَسَّطَتِ السَّمَاءَ انْتَشَرَتْ ثُمَّ أَمْطَرَتْ، فَلاَ وَاللَّهِ مَا رَأَيْنَا الشَّمْسَ سِتًّا، ثُمَّ دَخَلَ رَجُلٌ مِنْ ذَلِكَ الْبَابِ فِي الْجُمُعَةِ وَرَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَائِمٌ يَخْطُبُ، فَاسْتَقْبَلَهُ قَائِمًا فَقَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ هَلَكَتِ الأَمْوَالُ وَانْقَطَعَتِ السُّبُلُ، فَادْعُ اللَّهَ يُمْسِكْهَا عَنَّا‏.‏ قَالَ فَرَفَعَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يَدَيْهِ ثُمَّ قَالَ ‏"‏ اللَّهُمَّ حَوَالَيْنَا وَلاَ عَلَيْنَا، اللَّهُمَّ عَلَى الآكَامِ وَالظِّرَابِ وَبُطُونِ الأَوْدِيَةِ وَمَنَابِتِ الشَّجَرِ ‏"‏‏.‏ قَالَ فَأَقْلَعَتْ وَخَرَجْنَا نَمْشِي فِي الشَّمْسِ‏.‏ قَالَ شَرِيكٌ سَأَلْتُ أَنَسَ بْنَ مَالِكٍ أَهُوَ الرَّجُلُ الأَوَّلُ فَقَالَ مَا أَدْرِي‏.‏
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya shiga masallaci a ranar Juma'a ta wata ƙofar da ta kasance daura da gidan hukunci, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsaye, sannan ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya shayar da mu, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah Ka shayar da mu» Anas ya ce: Na rantse da Allah bama ganin wani girgije ko wani yanki na girgije kuma tsakaninmu da Sal'a babu wani ɗaki ko gida, ya ce: Sai wani girgije ya ɓullo ta bayanmu kwatankwacin garkuwa, lokacin da ya tsaya a tsakiyar sama sai ya yaɗu, sannan ya zubar da ruwa, na rantse da Allah, bamu ga rana ba tsawon kwana shida, sannan wani mutum ya shigo daga waccan ƙofar a wata Juma'ar, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana tsaye yana huɗuba, sai ya fuskance shi a tsaye, sai ya ce: Ya Manzon Allah, dukiyoyi sun halaka, hanyoyi sun yanke, ka roƙa mana Allah Ya ɗauke mana ruwan, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ɗaga hannayensa, sannan ya ce: «Ya Allah Ka saukar da ruwan a gefenmu ba akanmu ba, ya Allah akan tuddai da duwatsu, da cikin kwarrai, da matsirar bishiyoyi» ya ce: Sai ya ɗauke, sai muka fita muna tafiya cikin rana, Sharik ya ce: Na tambayi Anas ɗan Malik: Shin shine mutumin nan na farko? sai ya ce: «Bansani ba».

Fassara: HadeethEnc.comSharhinsa

Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.

Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.

Littafi na 15 · Invoking Allah for Rain (Istisqaa)

Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.