Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW ya kasance idan ya xago da kansa daga Raka'ar Qarshe, yana cewa: "Allah ka kuvutar da Ayyash Bn Abi rabi'a Ya Ubanhiji ka kuvutar da Sakamah Bn Hisham Ya Ubangiji ka kuvutar da Al-walid Bn Alwalid, Ya Ubangiji ka kuvutar da raunanan Muminai, Ya Ubangiji ka tsananta Kamunka ga Mudhar, Allah ka sanya musu yinwa kamar Shekarun Annabi Yusuf" Kuma cewa manzon Allah SAW ya ce: "Ghifar Allah ya gafarta mata" Ibn Abi Al-zinad ya ce daga Babansa: Wannan baki xayan sa a Asuba ne
Tushen bai rubuta wata daraja ga wannan ruwaya ba.
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.