Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Sahih Bukhari (881) Sahih Muslim (850)Zubair Ali Zai
Inda Insakulofidiyar Hadisan Annabi da aka Fassara (HadeethEnc.com) take da ainihin rubutun wata ruwaya, ana nuna fassararta a ƙarƙashin wannan ruwayar tare da sunan tushen. An haɗa su biyun ne ta hanyar shiri, daga Larabcin kaɗai: dukan rubutun hadisin da ke cikin insakulofidiyar, tare da sunan Sahabin da ya ambata, shi ne ƙarshen ruwayar harafi da harafi. Babu wanda ya bincika wannan haɗin, kuma masu bitar Sabīl ba su duba fassarar ba. Larabcin shi ne rubutun.
Rubutun Larabci, lambobi, sunayen littattafai da darajoji ana nuna su daidai yadda suke a cikin wani buɗaɗɗen tarin bayanai (hadith-api). Sabīl bai tabbatar da daidaitonsa ko haƙƙoƙinsa ba tukuna, kuma ba a fara bitar malamai a kansa ba. Kafin lokacin, ku kwatanta ruwaya da bugaggen littafi kafin ku dogara da ita.